Ta hanyar sauya dokarta a ranar 7 ga Oktoba, sojojin Isra'ila sun ba da damar kwamandojin su yi kisan kiyashi a Gaza
Jaridar New York Times ta bayyana a cikin wani rahoto a ranar Alhamis (26 ga watan Disamba 2024) cewa sojojin Isra'ila sun canza ka'idojin yaƙi a farkon yakin Gaza a ranar 7 ga Oktoba, 2023, ta yadda kwamandojin wannan gwamnatin su ba da umarnin kai hari kan wasu wurare duk da yiwuwar kashe fararen hula a wadannan wurare.
An bayar da wannan umarni na sojojin yahudawan sahyoniya da nufin cewa kwamandojin na Isra'ila na iya kai hari ga kwamandojin Hamas a lokacin da suke tare da iyalansu.
Jaridar New York Times ta bayyana cewa, ta shirya wannan rahoto ne bisa hirarrakin da aka yi da sojoji da jami'an gwamnatin Sahayoniyya fiye da 100 da kuma wasu mutane sama da 25 da ke da hannu wajen zabar wuraren da za a kai harin.