A cewar tashar Tasnim, majiyoyin Isra'ila sun ruwaito da sanyin safiyar yau Juma'a cewa, an yi ta jin karar gargadi a manyan yankunan Falasdinu da aka mamaye daga hamadar Negev zuwa Tel Aviv.
Jim kadan bayan haka, kafofin yada labarai na yaren yahudanci sun ba da rahoton cewa, an harba makami mai linzami guda daya ko fiye daga kasar Yemen zuwa Tel Aviv kuma an kunna kayayyakin aikin tsaron sararin samaniyar Isra'ila.
Kungiyar "Red Star of David" (kungiyar agaji ta Isra'ila) ta sanar da cewa mutane 18 ne suka jikkata a safiyar yau a birnin Tel Aviv yayin da suke tserewa zuwa matsugunan saboda cunkoson jama'a.
A halin da ake ciki, sojojin Isra'ila mamaya sun kuma yi ikirarin cewa sun kai hari kan wani makami mai linzami na Yaman kafin shiga cikin yankin Falasdinun da aka mamaye.
Tashar talabijin ta Channel 12 ta Isra'ila ta bayar da rahoton cewa, filin jirgin sama na Ben Gurion ya dakatar da sauka da tashin jiragen sama na wasu lokaci.
Kakakin sojojin Yemen: Mun Kai Hari Kan Filin Jirgin Saman Ben-Gurion Da makami Mai Linzami
Birgediya Janar Yahya Saree, kakakin rundunar sojin Yaman:
A wani aikin soja mai inganci, mun kai hari filin jirgin sama na Ben-Gurion da ke yankin Yaffa da aka mamaye da makami mai linzami na Palestine-2.
Duk da boye-boye da makiya suka yi, wannan makami mai linzami ya yi nasarar kaiwa ga inda aka nufata, kuma wannan aiki ya yi sanadin asarar rayuka da dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a filin jirgin.
Hakanan kuma Sojojin saman Yaman sun kai hari kan jirgin ruwan Santa Ursula da ke gabar tekun Larabawa da ke gabashin tsibirin Socotri tare da wasu jirage marasa matuka, manufar kai hari ga wannan jirgin dai shi ne saboda kamfanin da ya ke da shi ya karya matakin hana shiga tasoshin ruwa na Falasdinu da aka mamaye. Aikinmu ba zai tsaya ba har sai an daina kai harin da ake kai wa Gaza, kuma an dage wannan kawanya.