Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

9 Disamba 2024

11:55:39
1512368

Bidiyoyin Yadda Isra'ila Ta Mamaye Garuruwa Biyu A Cikin Kasar Siriya

Amurka na sane da matakin da gwamnatin Sahayoniya ta dauka na mamaye wani yanki na kasar Siriya

Majiyoyin yada labarai sun bayyana masaniyar gwamnatin Amurka kan matakin da gwamnatin sahyoniyawan ta dauka na mamaye wani yanki na kasar Siriya.

Wadannan majiyoyin sun ce gwamnatin Amurka ba ta nuna adawa ko kin amincewa da wannan mataki na gwamnatin sahyoniyawan ba.

Gwamnatin Sahayoniya ta mamaye garuruwa 2 na Siriya

Kafofin yada labaran kasar sun ce sojojin yahudawan sahyoniya sun mamaye garuruwan Baath da Hadar da ke lardin Quneitra na kasar Siriya. Kafafen yada labarai sun bayar da labarin yunkurin da sojojin yahudawan sahyoniya suka domin zuwa birnin Daraa na kasar Siriya.

A halin da ake ciki kuma jaridar New York Times ta rubuta cewa sojojin kasa na gwamnatin Sahayoniya sun shiga kasar Siriya a karon farko tun bayan yakin Oktoban 1973.

Hakan na faruwa ne bayan faduwar gwamnatin Assad kuma duk da gargadin da Kungiyar kasashen Larabawa ta yi na cewa kar Isra'ila tayi amfani da wannan damar wajen keta iyakar da cin zarafia Syria

Kungiyar hadin kan Larabawa ta yi gargadi game da matakan wuce gona da iri na gwamnatin sahyoniyawan da kuma cin zarafin halin da ake ciki a kasar Siriya a halin yanzu, tare da jaddada cewa haramtacciyar kasar Isra'ila ta hanyar anfani da yanayin da ake ciki a kasar ta Siriya, ko a matakin mamaye wasu kasashe a yankin Golan da ko karya yarjejeniyar 1974 muna masu yin Allah wadai akan hakan.

Kungiyar kasashen Larabawa ta jaddada wajabcin kammala shirin mika mulkin kasar ta Siriya cikin lumana cikakkiya da aminci, tare da hadin kan yankunan kasar Syria da 'yancin kai da kuma yin watsi da tsoma bakin kasashen waje a cikinta.

Kungiyar tana mai rokon dukkan bangarorin da ke da sha'awar tabbatar da zaman lafiyar yanki da na kasa da kasa da su goyi bayan al'ummar Siriya don cimma wannan mataki na rikon kwarya da kalubale da suke fuskanta.