A cikin wata sanarwa da rundunar sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta fitar ta sanar da shahadar mayakanta 4 a hare-haren na daren jiya.
Sakon wannan sanarwar shine kamar haka:
سْمِ اللَّـهِ الرَّحْمَـٰنِ الرَّحِيمِ
مِنَ الْمُؤْمِنِينَ رِجَالٌ صَدَقُوا مَا عَاهَدُوا اللَّهَ عَلَيْهِ فَمِنْهُمْ مَنْ قَضَى نَحْبَهُ وَمِنْهُمْ مَنْ يَنْتَظِرُ وَمَا بَدَّلُوا تَبْدِيلاً
Da sunan Allah, Mai rahama Mai Jinkai
Daga cikin muminai akwai mazaje da suka cika abin da suka wa Allah alkawari da shi, saboda haka daga cikinsu akwai wadanda lokacinsu ya kare daga cikinsu kuam akwai wadanda suke jiran lokacinsu amma kuma basu canja ko kadan.
Sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun sadaukar da sojojinsu 4 a daren jiya a lokacin da suke tunkarar harin gwamnatin sahyoniyawa masu laifi domin kare tsaron kasar Iran da kuma kare cutar da al'umma da kuma maslahar kasar Iran.
Za a fitar da ƙarin bayani nan ba da jimawa ba.
An buga hotunan shahidan sojoji a harin da gwamnatin Sahayoniya ta kai
Manjo Jahandideh da Istiwar Shahrokhifar da Muhammad Mahdi da Sarkar Sajjad Mansori sune shahidan da sukai shahada a harin da gwamnatin sahyoniya ta kai Iran.