Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Asabar

19 Oktoba 2024

06:35:12
1496007

Hizbullah Ta kai Hari Gidan Da Netanyahu Ke Zaune Da Jirgi Marar Matuki

Majiyoyin yahudawan sahyoniya sun sanar da kutsawa tare da saukar wani jirgin mara matuki daga kasar Labanon a yankin Kaisariya (gidan Netanyahu).

Bayan saukar wanna jirgi jami'an tsaro da agaji na gwamnatin sahyoniyawan a birnin Kaisariya da gidan Netanyahu, sunyi gaggawar kai dauki bayan harin da jirgin saman Hezbollah na kasar Labanon ya kai.

Kamar yadda muka sani Gwamnatin yahudawan sahyoniya ba ta yarda a buga irin hasarar rayukan da aka yi a yankunan da aka mamaye tare da tsauraran labaran karya ba, amma wata kafar yada labarai ta sahyoniyawan da ba ta hukuma ba ta bayar da rahoton cewa, wani jirgi mara matuki ya afkawa gidan Netanyahu, wanda ba za a iya tabbatarwa ko rashin hakan.

Wannan tasha ta gwamnatin sahyoniya ta ce sake gina gidan Netanyahu ba ya bukatar amincewar babban mai shari'a.

Ba da dadewa ba Netanyahu ya bukaci a sake gina gidansa, kuma ofishin mai shigar da kara na Isra'ila ya nuna adawa da hakan, amma da alama sake gina gidansa na da tabbacin faruwar lamarin a safiyar yau.

Shafin Qatar Arab ya ruwato cewa: Jirgin Hezbollah mara matuki ya kai hari ne kaitsaye ga gidan Netanyaho

Kamfanin dillancin labaran Al-Arabi na kasar Qatar ya habarta cewa, wani jirgin mara matuki da kungiyar Hizbullah ta harba zuwa yankin Qaisaria ya afkawa gidan Netanyahu.

Sojojin yahudawan sahyoniya sun tabbatar da cewa wannan jirgi mara matuki ya afkawa wani gini a yankin Qaisariyeh.

Kafofin yada labaran Isra'ila ba su buga wani hoto na wurin da aka harba wannan jirgi maras matuki ba.