Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Alhamis

17 Oktoba 2024

21:02:22
1495722

Bidiyon Da Na'urar Quadcopter Isra'ila Ta Naɗa Dale Nuna Lokacin Da Aka Kashe Shahid Sinwar

Yayi ta fafatawa har zuwa lokacin karshe...Yahya Sinwar ya fafata har zuwa minti na karshen rayuwarsa.

Kamar yadda kafafen yada labarai na Ibraniyawa suka fitar; Sojojin Isra'ila sun hango mayakan Hamas da dama a yayin da suke gudanar da ayyukansu a Rafah da ke kudancin zirin Gaza. Sannan suka umarci tankunansu da su bude wuta kan wadannan mayakan.

Duk mayaƙan sun mutu in banda mutum ɗaya wanda shi ne Yahya Sinwar. Don haka sojojin Isra'ila sun harba makamin roka mai fashewa da ake harba shi akan kafada zuwa ginin, wanda kuma shima bai yi nasarar kashe Sinuwar ba.

Bayan haka sojojin sun harba jirgin FPV maras matuki a kan Sinwar, wanda ya Sinwar ya tsaya, ya tattara wasu duwatsu da sanduna, yana mai kokarin harbo jirgin.

Bayan haka, bayan fiye da mintuna 15, wani maharbin cikin tankar yakin sojojin Isra'ila ne ya harbe Yahya Sinwar a kai, ya kuma yi amfani da jirgin mara matuki a lokacin da baya da wani kariya. Wannan ya bayyana raunin harsashin da aka gani a cikin hotuna. Ya yi yaƙi har zuwa lokacin ƙarshe.

Ku kula da faifan bidiyon, an datse hanny daya daga cikin hannayen shahidin kafin shahadarsa kuma ahakan ci gaba da gwagwarmaya a cikin mawuyacin hali.

A wannan hoton bidiyon, zamu ga Al-Sinwar ya samu rauni kuma ya kasa motsi.

Kafofin yada labaran Isra'ila sun tabbatar da cewa wani soja ya samu munanan raunuka yayin wani artabu da Yahya Sinwar a Rafah da ke kudancin zirin Gaza.

Jaridar Hebrew ta Ha'aretz: Bincike na farko ya nuna cewa Sinwar ya yi artabu da sojojin Isra'ila kuma yana mai jefa musu gurneti.