Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Laraba

5 Yuni 2024

19:52:12
1463533

Ci Gaba Tattaunawar Shekh Zakzkay (H) Da Wakilan Kamfanin Labarai Na ABNA

Shekh Zakzaky: Sakona Zuwa Ga Dukkan Musulmi Shi Ne Su Manta Da Sabanin Da Ke Tsakaninsu, Su Sani Cewa Suna Da Lamari Kwara Guda Ne Dubi Halin Da Ake Ciki A Gaza

Manzon Allah (S.A.W) ya ce a cikin ruwaya cewa Musulmi kamar jiki guda ne cewa idan wani bangare ya yi ciwo to sauran sassan ma za su yi ciwo. Sai dai kash, mu musulmi mun rabu, kuma ya zama dole mu manta da batun bangaranci, mu tuna cewa mu al’umma daya ce, masu lamari daya. A daya bangaren kuma, muna ganin makiya duk da ra'ayoyi mabanbanta da suke da, amma sun tsaya kan layi daya, sun hada kai don fuskantar musulmai.

Abna: Bayan Juyin Juya Halin, Da Yaushe Ne Haduwarku Ta Farko Da Imam Khumaini (RA) Ta Kasance?

Bayan nasarar juyin juya halin Musulunci, haduwata ta farko da Imam Khumaini (RA) ta kasance a Iran. Wannan ganawar ta faru ne a lokacin da Imam Rahel yake kwance a asibiti. Ganawata ta biyu da Imam Khumaini (RA) ta faru ne a lokacin da na je wajen Husainiyyar Jamaran yayin ganawar Imam Rahel da jama’a, sannan bayan wannan ganawar na gana da Imam Khumaini (RA) a cikin gidansa.

Abna: Wane Siffofi Ne Na Imam Khumaini (RA) Ta Zama Darasi Gare Ku?

Imam Khumaini ya kasance alama ce ta haƙiƙanin Musulunci, ba alama ce ta addini ko ƙungiya ba. Wasu malamai suna kiran mutane zuwa ga darika ko wata kungiya kwara daya, amma kiran Imam Khumaini (RA) ya kasance na Musulunci kuma bai yi kira zuwa ga wata mazhaba ba, sai dai ya dauki dukkan musulmi a matsayin al'umma daya, kuma ya dauki cewa nauyin daya hau kansa shine ganin wadanda aka zalunta a duniya sun samu ‘yanci. hakan ya sanya dukkan mutane daga mazhabobi da addinai daban-daban suka shaku da Imam Khumaini (RA).

Abna: Ku Yi Mana Bayani Kan Yanayin Ayyukan Wa’azinku A Najeriya

Idan za’a ce za je kasar Ahlus-Sunnah ka gaya wa mutanen can cewa mu ne muke da mazhabar gaskiya, ku zo garemu, to babu wanda zai zo wurinka. A kasar Najeriya akwai mazhabobin addini daban-daban, musamman ma ta Malikiyya, kuma darikun Sufaye daban-daban ne ke gudana a wannan kasar, kuma Wahabiyawan Najeriya suna kafirta mabiya wadannan darikun Sufayen. Mu Mun fadawa musulman Nigeria cewa mu musulmai ne kuma muna da al'amari daya a gabanmu wato "musulunci" kuma musulunci ya hada mu baki daya. Wannan shi ne abin da muke muhawara da su kenan.

Sa’ad da mutane suka zo wurinmu, suna ganin abin da ba su sani ba, misali, yadda muke yin sallah. Haka nan, muna gayyatar jama’a a Nijeriya da su halarci tarukan addu’o’inmu kamar karatun Du’au Komel ko su halarci tarukan addini da muke gabatarwa irinsu taron Maulidin Manzon Allah (SAW) har su saurari jabawanmu. Sannan su da kansu su fara bincike don gano gaskiyar lamarin. Salon Hanyar wa’azinmu tana da amfani sosai kuma hakan ya jawo mutane zuwa gare mu har da Kiristoci.

Abna: Wane Irin Zarge-Zarge Ne Ake Maku?

Shekh Zakzaky: Zagin Sahabbai na daga cikin zargin da makiyanmu suke yi mana, amma mu bama masu martani akai, mukan ce ne mu dukkan mu Musulmai ne, ku zo wajenmu ku ga hakikanin gaskiya da kanku daga garemu ba daga wajen makiyanmu ba, Yayin da suka zo wurinmu sai suka ga yadda muke mu’alantarsu, hakan ya janyo su garemu. Mun koyi wannan hanyar wa'azin namu daga Imam Imam Rahal Rh bai ce ku zo ku bi wani mazhaba ba, sai dai ya ce mu duka musulmi ne, kuma ya zama wajibi mu yi aiki domin Musulunci.

Abna: Bayan Shekarun Zaman A Kurkuku Da Gwagwarmaya Da Kuka Sha, Yaya Kuka Ji Game Da Sake Tafiyarku Zuwa Iran?

Shekh Zakzaky: Ina godiya ga gwamnati da al'ummar Iran bisa wannan gagarumin tarba na maraba da aka yi min kuma hakan ya nuna irin kaunar da Iraniyawa suke yi min. A Nijeriya mun bi makarantar Imam Khumaini (r.a) kuma har yanzu muna bin wannan makaranta da Jagora ke jagoranta a halin yanzu.

Abna: Bisa La’akari Da Abubuwan Da Ke Faruwa A Duniyar Musulunci A Baya-Bayan Nan; Musamman Dangane Da Falasdinu Da Gaza, Wane Irin Nuni Ko Sako Da Kuke Da Shi?

Shekh Zakzaky: Sakona zuwa ga dukkan musulmi shi ne su manta da sabanin da ke tsakaninsu, su sani cewa suna da lamari kwara guda. Dubi halin da ake ciki a Gaza a yau inda dubban mutane suka yi shahada kuma galibin wadannan shahidan mata ne da kananan yara. Sai dai abin bakin cikin shi ne wasu musulmi nawa lamarin kallo da mahangar bangaranci addini, kuma duk mai goyon bayan al'ummar Palastinu suna cewa ya yi hakan ne da wata manufa ta bangarancin addini ne, ba tare da ganin cewa lamarin Palastinu lamari ne na Musulunci ba gaba daya, mu musulmi ne al'umma daya ce mu.

Manzon Allah (S.A.W) ya ce a cikin ruwaya cewa Musulmi kamar jiki guda ne cewa idan wani bangare ya yi ciwo to sauran sassan ma za su yi ciwo. Sai dai kash, mu musulmi mun rabu, kuma ya zama dole mu manta da batun bangaranci, mu tuna cewa mu al’umma daya ce, masu lamari daya. A daya bangaren kuma, muna ganin makiya duk da ra'ayoyi mabanbanta da suke da, amma sun tsaya kan layi daya, sun hada kai don fuskantar musulmai.