Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

3 Yuni 2024

19:26:36
1463149

Ci Gaba Da Tarihin Imam Khumaini Qs

Rayuwar Imam Khumaini Rh A Lokacin Gwagwarmaya

Ruhin gwagwarmaya da jihadi a tafarkin Allah ga Imam sun samo asali ne daga hangen nesa na addini da tarbiyyar iyalan Imam Khumaini (AS) ke da shi. Ya fara gwagwarmayarsa tun yana dan saurayi kuma ta samu ci gaba daa bunkasa daidai da yanayin ruhi da na iliminsa, a wani bangare guda bisa tasiri da yanayin siyasa da zamantakewa na Iran da sauran al'ummar musulmi a wani bangaren kuma yanayin gwagwarmayarsa taci gaba ta fuskoki daban-daban. A farkon shekara ta 1300HS.

Ruhin gwagwarmaya da jihadi a tafarkin Allah ga Imam sun samo asali ne daga hangen nesa na addini da tarbiyyar iyalan Imam Khumaini (AS) ke da shi. Ya fara gwagwarmayarsa tun yana dan saurayi kuma ta samu ci gaba daa bunkasa daidai da yanayin ruhi da na iliminsa, a wani bangare guda bisa tasiri da yanayin siyasa da zamantakewa na Iran da sauran al'ummar musulmi a wani bangaren kuma yanayin gwagwarmayarsa taci gaba ta fuskoki daban-daban. A farkon shekara ta 1300HS, lokacin da Ridha Khan ya so ya wargaza Makarantar hauza ta birnin Qum ta hanyar bayar da umarnin gudanar da jarrabawar kasa ga malaman addini, Imam Khumaini ta hanyar bayyana manufofin wanna yunkuri na bayan fage ya nuna adawa da hakan. Ya kuma gargadi wasu mashahuran malaman Kum wadanda suke da sassaukan tunani da suke daukar wannan mataki a matsayin wani mataki na gyarawa.

A lokacin Marja’iyyar Ayatullah Burujardi, Imam ya kasance mamba a kwamitin kawo sauyi wanda ke da manufar kawo sauyi da gyara a Hauz. Ayatullah Burujardi yana shawartarsa akan batutuwa daban-daban, musamman batutuwan da suka shafi gwamnati. Bayan kama mutanen da ke da hannu a kisan Husain Alaa firaministan kasar A shekara ta 1329, ya je ya gana da Shah a madadin Ayatullah Burujardi don hana aiwatar da hukuncin kisa kan wadannan mutanen.

A shekara ta 1322 ta hanyar rubuta littafin Kashf Asrar, ya fallasa masifofin mulkin Pahlawi na shekaru ashirin kuma domin kare Musulunci da malaman addini a amsa tare da bayar da martani ga shubuhohi da farmakin masu karkatattun tunani, kuma a cikin wannan littafin dai ya bayyana nazariyyar gwamnatin Musulunci da wajabcin tsayar da ita. Bayan an yi shekara guda a cikin rudani da yanayi na sakewa bayan Ridha Pahlawi, Imam ya yi jawabinsa na farko na siyasa inda ya kira malaman Musulunci da al'ummar musulmi zuwa ga wani yunkuri na gaba daya.

A watan Mihr na shekara ta 1341, gwamnati ta amince da kudirin doka na jihohi da na larduna, wanda acikinsa kudirin aka share sharudda guda uku na farko zama musulmi, da yin rantsuwa da littafin Allah da kuma ya zamo dan takarar zabe namiji ne, domin a samar da dama ga Baha’iyyawa samun tarayya a ciki. Imam a cikin telegraf zuwa ga Asadullah Alam ya rubuta cewa: “Ina sake yi maku nasiha da ku yi biyayya ga Allah Madaukakin Sarki da tushen Kundin Tsarin Mulki, kuma ku ji tsoro da guje wa munanan sakamakon da zai biyo na sabawa Kur’ani da hukunce-hukuncin malaman Al’umma da shugabannin musulmai tare da tsoron keta shari’a. Kuma kada ku jefa kasar cikin hatsari ba tare da dalili ba; saboda malaman Musulunci ba za su daina bayyana ra’ayinsu game da kai ba”. Sakon Imam mai karfi ya ya zamo na musamman mara tamka a yanayin wannan lokacin.

Imam Khumaini Da Yunkurin 15 Khurdad

Imam Khumaini ya bayyana a matsayin jagoran juyin juya halin Musulunci a shekara ta 1342, wanda ya zamoa shekaru masu yawa kafin haka, ya shiga matakai daban-daban na inganta kansa da tsarkake kansa, da jihadi mai girma, da samun kyawawan halaye na ruhi da ilimi na hakika a mafi girman matsayi. Ya dauki inganta kai da jihadi na tsaftace ran mutum a matsayin abu mafifici a kan gwagwarmayar waje ta bayyane, har ma ya ce koyan ilimomi daban-daban da ilimin tauhidi, idan ya zamo ba a tare da tsabtar ruhi ba, ba wani abu zai zamo ba face burunburun ba kuma ba zai kai ga hakikar gaskiya ba.

Jim kadan bayan hayaniyar kungiyoyin jiha da na larduna, Shah ya ba da sanarwar zaben raba gardama kan wani aiki mai suna farin juyin juya hali. Shi kuma Imam a cikin bayyanannun bayanan kwanaki hudu kafin gudanar da zaben raba gardama, ya dauki farin juyin juya hali da tanade-tanade da suka hada da gyaran kudi da cewa sun sabawa Musulunci da Kundin Tsarin Mulki. A cikin bayanin nasa na tarihi ya ce: “Ina ganin mafita a cikin wannan, cewa wannan gwamnati mai ci ta ja da baya saboda laifin keta dokokin Musulunci da keta haddin tsarin mulki; Sannan kuma gwamnatin da ta yi riko da dokokin Musulunci da ta ke damuwa da damuwar al'ummar Iran ta tazo.

Bayan yaduwar zanga-zangogi’ bisa umarnin gwamnatin Pahlawi, jami'an da ke dauke da makamai cikin sauyin kaya a boye suka kai hari a makarantar Faidhiyah a watan Farvardin 1342 tare da kashe dalibai tare da raunata su. Bayan wannan harin, a ranar 31 ga Farvardin 1342, Imam ya watsa shelarsa da ta shahara mai taken: "Shahdusti ya’ni garatgari" ma’ana ( Abota da sarki yana nufin kar farmaki). A cikin wannan sanarwa, wacce take daya daga cikin maganganun siyasa mafi kaifin ta Imam Khumaini, an gurfanar da gwamnatin Shah a gaban shari'a, kuma a karshenta an jaddada cewa takiyyah haramun ce a cikin wadannan yanayi kuma bayyana hakikanin lamarin yadda yake gudana wajibi ne.

A wani yanayin da SAVAK ya yi alkawari daga masu jawabi na cewa ba za a tona asirin Shah da Isra'ila ba, Imam ya yi kakkausar suka kan tsoma bakin Shah da Isra'ila a jawabinsa na Ashura 1342. A cikin daren ne aka kama Imam aka kai shi daga Kum zuwa Tehran. Amma tare da boren mutanen Tehran da Waramin da kuma matsin lamba na malamai ya sa gwamnati ta sake shi.

Rashin Amincewar Imam Khumaini Na Yin Kaura Da Gudun Hijira Zuwa Turkiyya

 

21 ga watan Mihr 1343 An amince da kudurin dokar a zauren majalisar bisa ga wannan kudiri, Iran ta ba wa masu ba da shawara kan sojan Amurka damar cin gajiyar samun kariya da kulawa da aka kawo a cikin yarjejeniyar Vienna, kamar jami'an diflomasiyya da ma'aikatan gudanarwa da fasaha na ofisoshin jakadancin. A cikin wannan lamari Imam ya kuduri aniyar cika sakonsa na tarihi kuma yi qudirn sake sabon yunkuri. A cikin tarihin Imam Khumaini an bayyana cewa ya zabi ranar hudu ga watan Aban wato ranar haihuwar Shah a matsayin ranar bayyanawa kuma ya isar da labarin hakan zuwa ga malaman garuruwa daban-daban. Duk da irin barazanar da ake yi, Imam ya nuna rashin amincewa da kudirin yan jari hujja a cikin shahararren jawabinsa na ranar 4 ga watan Aban. A cikin wannan jawabi ne Imam ya fadi shahararriyar jumlarsa kamar haka; Amurka ta fi Ingila muni, Ingila ta fi Amurka muni, Tarayyar Soviet ta fi su duka. Dukkansu mafi muni ne; Dukkan mafi muni ne fiye da junansu. Amma a yau muna fama da wannan mummunar! tare da Amurka. Ya kamata shugaban Amurka ya sani - ya san wannan ma'anar - cewa shi ne wanda aka fi kyama a duniya a wajen al'ummarmu... duk matsalolinmu daga wannan Amurkar ne! Dukan wahalarmu daga wannan Isra'ilar ne! Daga Isra'ila kuma daga Amurka.

Tona asirin da Imam ya yi a kan amincewar daftarin kudirin doka ya sanya Iran a gab da sake yin wani bore a watan Aban 1343; Amma gwamnatin Shah ta yi amfani da damar da ta samu na murkushe yunkurin 15 na Khurdad na shekarar da ta gabata, kuma cikin sauri ta dauki mataki tare da yanke shawarar korar Imam Khumaini. Bisa umarnin gwamnatin Pahlawi, an kama Imam Khumaini ne a ranar 13 ga watan Aban tare da jinkirin 'yan kwanaki saboda gudanar da zaben shugaban kasar Amurka, aka kuma kore shi zuwa Turkiyya. Zaman Imam Khumaini a Turkiyya ya kai tsawon wata goma sha daya.

Imam Khumaini A Lokacin Hijira A Najaf

A ranar 13 ga Mehr shekara ta 1344 ne aka aike da Imam da dansa Haj Agha Mustafa daga kasar Turkiyya zuwa waje na biyu na gudun hijira a kasar Iraki. Daga lokacin da Imam Khumaini ya isa birnin Najaf ya ci gaba da raya alakarsa da masu gwagwarmaya ta hanyar aikewa da wasiku da 'yan sako zuwa kasar Iran tare da kiransu da su jajirce wajen cimma manufofin yunkurin 15 Khourdad. Kamar yadda ya zo a tarihin rayuwar Imam Khumaini, ya fito fili ya yi magana game da bore mai girma na siyasa da zamantakewa da ke gabatowa a Iran. A ranar 27 ga Farvardin 1346, ya rubuta a cikin wani sako da ya aike wa makarantun hauza na Iran cewa: “Ina tabbatar muku ya ku ma’abota girma da kuma al’ummar Iran cewa tsarin zai fuskacin rashin nasara. Magabatansu sun sha marin Musulunci, su ma za zasu sha nasu marin... ku jajurce. Kada ku mika wuya ga zalunci. Su din nan masu wucewa ne kuma ku zaku wanzu... Waɗannan dakusassun takubban zasu shude tsirara ba tare kube ba.

A wannan rana Imam Khumaini ya rubuta budaddiyar wasika zuwa ga firaministan kasar Shah, Amir Abbas Huwaida, inda ya lissafta irin masifun da gwamnatin kasar ta haifar tare da gargadi kan jan tanga da Shah yayi don yakar gwamnatocin Musulunci. Haka nan Imam ya koyar da darussa da dama na Durusul Khairij a lokacin da yake gudun hijira a Najaf, wanda ya ci gaba har zuwa lokacin da ya yi hijira zuwa birnin Paris duk kuwa da adawa da hargitsi na bangaranci. Harsashin da Imam ya kafa a fannin shari'a da ka'idoji da kuma yadda ya yi fice a fagen ilimin Musulunci ya tabbata akansu wanda kasance bayan wani dan lokaci kadan duk da’irar darussansa, an dauke shi a matsayin daya daga cikin fitattun masu bada darussa a Najaf ta fuskar inganci da na nagarta.

Kokari da wayewar Imam Khumaini ya canza yanayin Najaf tsawon shekaru hudu na koyarwa. A cikin tarihin Imam Khumaini an bayyana cewa a shekara ta 1348 baya ga masu gwagwarmaya da ba su da adadi a cikin kasar, akwai abokan hulda da dama a kasashen Iraki, Labanon da sauran kasashen musulmi wadanda suka dauki yunkurinsa a matsayin abin koyi. Don haka ne Imam ya fara jerin darussa na gwamnatin Musulunci ko kuma fikihu a Bahman 1348. An buga gungun jerin karatuttukansa ne a sigar littafi mai suna Wilayatul Faqih ko kuma gwamnatin Musulunci a Iran. A cikin wannan littafi, an fayyace mahangar gwagwarmaya da manufofin wannan yunkuri, sannan kuma an gabatar da hukunce-hukuncen Fikihu da na Usuli da na Falsafar hukunce-hukuncen Musulunci da kuma bahasin fahimta da suka shafi salon gwamnatin Musulunci daga harshen jagorancin juyin juya halin Musulunci.

Gwagwarmar Imam Khumaini A Najaf

Daya daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a zamanin da Imam ya zauna a Najaf, wanda ya yi tasiri matuka wajen yaduwar yunkurin Imam, shi ne yakin kwanaki shida na Larabawa da Isra'ila. Bayan wannan waki’ar a ranar 17 ga watan Khurdad 1346 ya bayar da fatawarsa ta juyin juya hali game da haramcin duk wata alaka ta kasuwanci da siyasa tsakanin gwamnatocin Musulunci da Isra’ila, da kuma haramcin cin kayayyakin Isra’ila a cikin al’ummomin Musulmi. Yunƙurin da duniyar musulmi ta yi a akan abunda ya faru a yaƙin Larabawa da Isra'ila ya haifar da damammaki ga Imam ya gabatar da manufofinsa a faɗaɗe, wanda shine farfaɗo da imani na addini a zamanin kin jinin addini da sake dawo da asalinsa da ɗaukakarsa da hadin kan al'ummar musulmi, kuma bai takaita a fada da Shah na Iran ba ne kawai. Imam Khumaini a wata tattaunawa da ya yi da wakilin kungiyar Al-Fath ta Falasdinu a ranar 19 ga watan Mihr 1347, ya bayyana ra'ayinsa kan batutuwan da suka shafi duniyar musulmi da kuma jihadin al'ummar Palastinu, kuma a cikin wannan hirar ya bayar da fatawa ta wajibcin ware wani bangare na kudaden Zakka na Shari'a ga mujahidan Palastinu. Zaku iya karanta rubutun hirar Imam da kungiyar Fatah.

A tsakiyar watan Isfand din shekarar 1353 ne sarki Shah ya dauki matakin kama-karya ta hanyar kafa jam'iyyar kotu ta "Restakhiz" tare da samar da tsarin jam'iyya daya, kuma a lokacin wani jawabi da aka watsa ta gidan talabijin ya bayyana cewa, ya kamata al'ummar Iran baki daya su zama mambobi a cikin wannan tsarin jam’iyya, kuma wadanda ba su amince da hakan ba, su samu fasfo dinsu su bar kasar nan take Imam ya fitar da fatawa da adawa da wannan kungiya da sabawarta ga Musulunci da maslahar al'ummar musulmi.

Wani abin da ya yi tasiri wajen yaduwar yunkurin juyin juya halin Musulunci shi ne shigar jam'iyyar Democrat cikin fadar White House a shekara ta 1355. Jimmy Carter ya yi nasara da taken haƙƙin ɗan adam da takaitawa kan fitar da makamai. An fitar da wadannan take-take ne da nufin hana ci gaban kyamar Amurka a kasashe irin su Iran, kuma sun kai ga bude wani yanayi mai ban mamaki da na wucin gadi na siyasa a Iran. Imam Khumaini wanda ya sanya ido sosai kan abubuwan da suke faruwa a duniya da Iran, ya yi amfani da damar da aka samu. Kamar yadda ya zo a cikin tarihin rayuwar Imam Khumaini, a cikin wani sako a watan Murdad 1356 ya bayyana cewa: Yanzu, saboda halin da ake ciki na ciki da waje da kuma yadda ake nuna laifukan tsarin mulki a majalisu da jaridu na kasashen waje wata dama ce da ya kamata majalisar ilimi da al'adu, mazan kishin kasa, daliban kasashen waje da na gida, da kungiyoyin Musulunci a ko'ina su yi amfani da shi nan take, su tashi tsaye a fili.

Shahadar Ayatullah Haj Agha Mustafa Khumaini a ranar farko ga watan Aban 1356 da kuma gagarumin taron da aka gudanar a kasar Iran shi ne mafarin sake yunkurin makarantun hauza da yunkurin al'ummar masu addini na Iran. Haka nan kuma Imam Khumaini cikin mamaki ya kira wannan lamari daga boyayyen ludufin Ubangiji. Gwamnatin Shah ta dauki fansa kan Imam ta hanyar buga labaran batanci ga Imam a cikin jarida. Zanga-zangar adawa da wannan rubutun jaridar ya haifar da boren Qum a ranar 19 ga watan Day 1356, inda aka kashe gungun masu neman juyin juya hali. Gudanar da taruka na uku da na bakwai da na arba'in a jere na tunawa da shahidan da suka yi boren baya bayan nan a garuruwan Tabriz, Yazd, Jahrom, Shiraz, Isfahan da Tehran ya haifar da bore da dama da suka haifar da ci gaba da yunkurin Imam Khumaini.

Daga lokacin da aka yi masa hijira zuwa Najaf har zuwa ranar 12 ga Mehr 1357, ya zabi ya zauna a can tsawon shekaru 12 da watanni 11. Lokacin da adawa da cin zarafi na tuntunben harsuka daga kowane bangare suka yadu masu ban haushi da cutarwa ta yadda Imam (RA) da dukkan hakuri da kauda kai amma yayi ta ambatar wahalar yanayin gwagwarmaya a wadannan shekaru, amma babu daya daga cikin wadannan wahalhalu da matsi da su ka iya karkatar da su daga kan hanyar da suka zaba cikin saninsu.

Hijira Imam Khumaini Zuwa Paris

A taron ministocin harkokin wajen kasashen Iran da Iraki a birnin New York, an yanke shawarar korar Imam Khumaini daga kasar Iraki. A shekara ta 1357, a wata ganawa da Imam Khumaini yayi da shugaban hukumar tsaron kasar Iraki ya bayyana cewa, sharadin ci gaba da zamansa a kasar Irakin shi ne ya daina gwagwarmaya kuma ya dena tsoma baki cikin harkokin siyasa. Amma Imam Khumaini ya amsa kai tsaye cewa ba ba zai yi shiru ko wani rangwame ba. A ranar 12 ga Mihr Imam ya bar birnin Najaf zuwa kan iyakar kasar Kuwait. Gwamnatin Kuwait ta hana Imam Khumaini shiga wannan kasa ta hanyar sa bakin gwamnatin Iran, don haka ne Imam ya yanke shawarar yin hijira zuwa birnin Paris. A ranar 14 ga watan Mihr suka isa birnin Paris suka sauka a gidan wani dan kasar Iran a Noufel Lochato (wajajen da ke wajen birnin Paris).

A zaman da Imam ya yi na tsawon watanni hudu a birnin Paris, Noufel Lochateau ta kasance cibiyar labarai mafi muhimmanci a duniya, kuma a tattaunawa da dama da tarurruka daban-daban na Imam ya bayyana ra'ayinsa kan gwamnatin Musulunci da kuma manufofin yunkurinsa nan gaba ga duniya. Ta haka ne mutane da yawa a duniya suka san tunaninsa da yunkurinsa.