Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

3 Yuni 2024

13:38:21
1463136

Kashi Na Farko

Tarihin Imam Khumaini (RA) ِDaga Haihuwa Zuwa Wafati

A cikin wannan takaittacen bayanin rayauwar, za ku karanta taƙaitaccen tarihin Imam Khumaini tun daga haihuwa har zuwa wafatinsa. wanda ya jagoranci juyin juya halin Musulunci na mutane a kan tsarin daular Shahansha tun daga shekara ta 1340HS. kuma matakin da Imam Khumaini ya dauka ga gwamnatin Pahlawi ne ya haifar da gagarumar zanga-zangar Al'ummar a shekarun 1356 zuwa 1357 bayan hijira, wanda a karshe ya haifar da nasarar juyin juya halin Musulunci na Iran.

          A cikin wannan takaittacen bayanin rayauwar, za ku karanta taƙaitaccen tarihin Imam Khumaini tun daga haihuwa har zuwa wafatinsa. (Ranar haihuwarsa a watan Shahrivar 1281HS). an haifi Imam a ranar 01 gawatan 07/ 1281HS. Imam ya kasance masanin fikihu, sufanci kuma marja’in Taqlidi abun koyi na Iran, wanda ya jagoranci juyin juya halin Musulunci na mutane a kan tsarin daular Shahansha tun daga shekara ta 1340HS. Imam ya hadu Kamu, gudun hijira, kuma matakin da Imam Khumaini ya dauka ga gwamnatin Pahlawi ne ya haifar da gagarumar zanga-zangar Al'ummar a shekarun 1356 zuwa 1357 bayan hijira, wanda a karshe ya haifar da nasarar juyin juya halin Musulunci na Iran.  

Iyalan Imam Khumaini Da Zuriyarsa

Agha Sayyid Mustafa (mahaifin Imam Khumaini) bayan kammala karatunsa na tushe a makarantun Khumaini tare da koyon harshen Larabci, ya ci gaba da karatu wana domin ci gaba da karatun a farko ya tafi Isfahan sannan ya tafi Najaf Ashraf. A Najaf Ashraf da Samarra ya zamo ya ci gaba da koyon karatunsa a karkashin kulawar Mirza Shirazi. Har ya zamo cikin malamai da mujtahidai na zamaninsa. Ya koma Khumaini a shekara ta 1273 HS. Kuma ya zama nauyin shugabancin al'ummar yankin Khumain, yayin da yake jagorantar al'umma ta hanyar ruhiyya, da mazahaba da addini, ya fara gwagwarmaya da zaluncin masu mulki da masu fada a ji da suke wa jama’ar wannan yankin. Ya yi kokarin hana cin zarafi da cin zalin da jami’an gwamnati ke yi wa jama’a. Wanda su kuma suna daukar Sayyid Mustafa a matsayin cikas a kan hanyarsu ta cimma burinsu da manufofinsu. A shekara ta 1281HS wanda acikin wannan shekarar cin zarafin hukuma ya karu a kan mutane, Sayyid Mustafa ya yanke shawarar sanar da gwamnan Iraki (Arak a yanzu) halin da ake ciki.

Biyu daga cikin masu shugabanni wadanda ke tsoron illar wannan rahoto, sun kai wa Agha Mustafa hari a tsakiyar hanyar Khumaini zuwa Iraki (Arak) ta hanyar harbinsa da bindiga a kahon zuciyarsa inda yayi shahada sakamakon wanna harbin.

Kakan Imam Khumaini (a.s) ana kiransa da Deen Alishah, wanda ya rayu a yankin Kashmir na kasar Indiya kuma yana daya daga cikin malaman Shi'a na wannan yanki. Kuma a can ne ya yi shahada. Sayyid Ahmad, wanda aka fi sani da Sayyid Hindi, dan Deen Alishah tsakanin shekara ta 1240 zuwa 1250HQ ya taso daga daga Kashmir ya nufi zuwa Atbat Aaliya kuma a lokacin da ya zauna a can ya samu sanayya tare da wani mutumin Khumaini mai suna Yusuf Khan Farfahani, daya daga cikin manya-manyan mutanen Khumaini. Bayan zurfafar wannan saninsa ga wannan mutumi me da aka ambata ya gayyaci Sayyid Ahmad kan ya zo Khumaini. Ya kuma amsa wannan gayyata

A shekara ta 1254HQ(1217HQ) domin ya shiryarwa da wa’azantar da mutanen Khumaini, sai ya isa garin kuma a ranar 17 ga Ramadan shekara ta 1257HQ ya auri 'yar Muhammad Husainbeg, wacce 'yar uwa ce ga Yusuf Khan. Sayyid Ahmad a karshen shekara ta 1285 zuwa 1286 bayan hijirar Qamariyya ya rasu. Kuma an kai gawarsa Karbala aka binne shi a cen. Auren Sayyid Ahmad ya haifar da albarkar 'ya'ya mata uku masu suna: Sultan Khanum, Sahiba Khanum da Aghabano da ɗa mai suna Sayyid Mustafa (mahaifin Imam Khumaini).

Tarihin Imam Khumaini Kafin Juyin Juya Halin Musulunci

Ya Rayuwar Imam Khumaini Ta Kasance A Lokacin Yarinta?

Shahadar mahaifinsa ta yi tasiri sosai a yarintar ​​Imam. Yayin da bai fi watanni biyar da haifuwar Imam Khumaini ba Tagutai da kuma wakilai da ke karkashin goyon bayan jami'an gwamnatin wancan lokacin suka shahdantar Agha Mustafa don ya tashi tsaye yana gwagwarmaya wajen tinkarar zaluncin da ake yi musu, su kuma azzalumai sai suka mayar da martani da harba harsasai suka shahadantar da shi a kan hanyar Khumaini zuwa Arak.

Bayan shahadar mahaifinsa Imam Khumaini ya yi yarinta a karkashin kulawar mahaifiyarsa (Sayyidah Hajara) da kuma innarsa mai daraja (Sahibah Khanum).

Ya yi karatu a makarantar Akhund Malla Abul Qasim. A wannan lokaci duk rana suna karantar rabin juz’i na Alqur'ani kuma karshen wannan gabar karatun suna kaiwa ga sauke Alqur'ani. Imam bayan ya kammala Alqur'ani yana dan shekara bakwai ya tafi wurin Sheikh Jafar domin koyon Larabci da adabi bayan na kuma ya tafi wajen Mirza Mahmud Iftikharul Ulama ya koyi karatu na tushen farko. Sannan ya fara karatun mataki na biyu tare da Mirza Mahdi - wanda shi ne kawunsa – sannan ya fara koyon karatun Mandiki a wajen Mirza Ridha Najafi. A cikin ci gaba da wadannan karance-karance da ake iya koyo a wannan mataki kamar: Mandiki, Kitab Mudauwal da Siyudi ya koye su a gun Ayatullah Murtadha Pasandideh (dan'uwansa).

Lokacin Samartarkar Imam Qs:

Samartakar Imam Khumaini ta fara ne da hijirarsa zuwa Arak da fara karatunsa a makarantar hauza a shekara ta 1330HS. Shi ya koyi karatun Mandik wurin Sheikh Muhammad Gulpaygani sannan ya karanci sharhin littafin Lum’ah a wajen Agha Abbas Araki. Watanni kadan basu wuce ba da shigarsa makarantar hauza ta Arak Ayatullah Sheikh Abdulkarim Haeri ya yi hijira zuwa wannan garin bisa bukatar malaman Qum inda ya kafa makarantar hauza ta Qum. kusan wata hudu bayan hijirar Ayatullah Haeri, shi ma Imam Ruhullah ya yi hijira zuwa Qum ya ci gaba da karatunsa a cen.

Imam Khumaini ya gama karanta karshen littafin Mudawwal a wajen Agha Mirza Muhammad Ali, wanda aka fi sani da Adib Tehrani, sannan ya koyi matsakaicin karatu a wajen Syyid Muhammad Taghi Khansari da Mirza Sayyid Ali Yasribi Kashaani, sannan ya shiga da'irar karatun Ayatullah Abdulkarim Haeri wanda ya yi karatun dukkan durusul Kharij a wajensa. Har ila yau Ya karanci falsafa a wajen Haj Sayyid Abulhasan Qazwini; sai Kuma Arudi da ilimin Qawafi da falsafar Garb da falsafar Takamul Darwin a wajen Sheikh Muhammad Ridha Esfahani Masjid Shahi; Ya koyi ilimin lissafi da Hai’at a wajensa da Mirza Aliakbar Yazdi da kuma sufanci a wajen Ayatullah Muhammad Ali Shahabadi.....