Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

2 Yuni 2024

06:54:48
1462870

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Zai Gudanar Da Jawabi Dangane Da Zagayowar Ranar Wafatin Imam Khumaini (Rh)

Za a gudanar da tarukan cika shekaru 35 da wafatin Imam Khumaini (Allah ya yi masa rahama) tare da halarta da kuma jawabin jagoran juyin juya halin Musulunci.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti (A.S) – ABNA – ya bayar da rahoton cewa: za a gudanar da tarukan cika shekaru 35 da wafatin Imam Khumaini (r.a) tare da halarta da kuma jawabin jagoran juyin juya halin Musulunci.

Wannan shiri da taro zai fara ne da safiyar ranar gobe litinin 14 ga watan Khordad 1403 wanda yayi daidai da 02 ga watan Yuni 2024 a hubbaren Imam Khumaini (RA) da karfe 8:00 na safe.

Jawabin da za’a gudanar a wajen taron yana daya daga cikin muhimman tarukan shekara shekara da jagoran juyin juya halin Musulunci yake yi tare da sauran al'ummar Iran da masu sha'awar juyin juya halin Musulunci da Imam Khumaini a duniya, wanda galibi yakan bayyana tushe da ka'idoji na makarantar Imam Khumaini (a.s) da muhimman batutuwan cikin gida da na waje .


Za a watsa wannan taro kai tsaye a kafar yada bayanai na KHAMENEI.IR da gidajen rediyo da talabijin na Jamhuriyar Musulunci ta Iran.