Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Jummaʼa

31 Mayu 2024

19:07:04
1462520

Ayatullah Ramezani: Rashin Gajiyawa Shi Ne Babban Halayen Shahidan Hidima

Cikakken Rahoton Taron Tunawa Da Shahidan Hidima Ayatullah Ramezani: Rashin Gajiyawa Shi Ne Babban Halayen Shahidan Hidima + Hotuna Da Bidiyo.

An gudanar da taron tunawa da girmamawa ga shahidan Hidima, taron wanda Majalisar Ahlul Baiti (AS) da Jami'atu Al-Mustafa Al-Alamiya (AS) na duniya suka gudanar a yammacin jiya Alhamis - 30 ga watan 05 2024 – wanda yyai daidai da 10 ga watan Khurdad 1403 tare da halartar wadanda: Malamai da manyan dalibai da malamai masu bincike wadanda ba Iranawa ba a birnin Qum.

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (A.S) ya habarta cewa, an gudanar da taron tunawa da shahidan hidima da majalisar Ahlul-baiti (A.S) da jami'ar Al-Mustafa Al-Alamiya suka gudanar a yammacin jiya Alhamis 30 ga watan 05 2024 – wanda yyai daidai da 10 ga watana Khurdad 1403 tare da halartar wadanda: Malamai da manyan dalibai da malamai masu bincike wadanda ba Iranawa ba a dakin taro na Quds da ke Mujtama’i Jami’i Imam Khumaini (RA) a birnin Qum.

A cikin wannan taro da ya samu halartar malamai da dalibai da malamai daga kasashen duniya daban-daban, Ayatullah Ramazani babban sakataren majalisar duniya ta Ahlul Baiti (AS), Dr. Abbasi, shugaban Jami’ar Al-Mustafa Al-Alamiya, da Hujjatul Islam Wal Muslimeen Al-Daqqah daga cikin malaman Bahrain, sun gabatar da jawabai.

Shahidan Hidima Sun Samu Horon Tarbiya Ne A Makarantar Ahlul Baiti (As)

A cikin wannan taro, Ayatullah Riza Ramazani ya yaba da irin muhimman ayyukan shahidan hidima yana mai cewa: An horar da shahidan hidima a makarantar Imaman juyin juya halin Musulunci, wacce ta samo asali daga mazhabar Ahlul Baiti (AS).

Babban sakataren Majalisar Ahlul Baiti (a.s.) ya kara da cewa: Imam Khumaini (RA) ya kasance yana cewa: An ciro ma’anar yunkuri guda biyu daga ayar mai daraja da take cewa: " «أَنْ تَقُومُوا لِلَّهِ مَثْنَىٰ وَفُرَادَىٰ..»". Daya shi ne yunkuri na daidaiku don tauhidi, daya kuma yunkuri ne na al'umma don tabbatar da shari'a, wanda shi ne adalcin da ya kasance fatawar dukkan annabawan Ubangiji. Don haka, don samun adalci a cikin al’umma, dole ne a biya farashi mai tsada. Imam Khumaini (RA) ya horar da dalibansa ta wannan hanya, shahidai irin su Shahid Bihishti da kuma a yau kamar Ayatullah Raisi, wanda kowannensu ya bar tasirin zamantakewa a cikin al'umma. Abin da aka iya samu a samuwarsu shi ne babban jari na zamantakewar al'umma na duniya. Wannan babban jari na kasa da kasa da aka samu albarkacin jinin shahidai, kamata ya yi a kiyaye shi da kuma amfani da shi wajen gudanar da yin zabe.

Shahidan Hidima Sun Kasance Masu Hidimtawa Mutane Na Hakika

Ayatullah Ramazani yana ganin cewa kasancewa a mai hidima ga mutane a matsayin daya daga cikin sifofi na musamman da shahidai suke da ita a kan tafarkin hidima ya kuma kara da cewa: A tsarin masu sassaucin ra'ayi ba a maganar halayya tare da siyasa, amma Shahid Raisi ya hada wadannan siffofi  aguri guda daya. A can wajensu, yin maganar ikhlasi a fagen siyasa ba shi da ma’ana, suna ganin ba shi da ma’ana ko da a fagen yada labarai ne; saboda haka ba a iya ganin wadannan koyarwar sai a cikin makarantar wahayi da makarantar Musulunci da mazhabar Ahlul Baiti (a.s.) cewa mutum dole ne ya so mutane, kamar yadda Amirul Muminin (a.s.) ya ce wa Malik Ashtar: “Ka so mutane. ." A mazhabar Ahlul Baiti (a.s.) da kuma mazhabar Imaman juyin juya halin Musulunci, za ka ga cewa ana yin aiki domin Allah ne kuma wannan yana daga cikin muhimman koyarwar Ahlul Baiti (a.s.). Ya tabbata a siyasar Musulunci cewa dan siyasa ya zama mai halin kirki, ma'auninsa ya zama gamsar da mutane da magance matsalolinsu, ya zamo bakin cikin mutane ya zama bakin cikinsa, farin cikin  mutane ya zama farin cikinsa.

Shugaba A Tsarin Musulunci Ya Zamo Bai San Gajiya Ba:

Haka nan kuma ya yi ishara da maganar da Jagoran juyin juya halin Musulunci da ya yi na cewa: “Raisi Aziz, bai san gajiya ba” ya ce: shugaba a tsarin Musulunci bai san gajiyawa ba, domin yana aiki ne ga Allah; Abin da ake nufi da gajiya ba gajiyawar jiki ba ce, domin a karshe jiki yakan gaji, amma ana nufin gajiyawar tunani ne. Tabbas ya zo a cikin riwayoyinmu cewa gajiyawar hankali da karaya suna da tasiri a yawancin cututtuka na zahiri na jikin mutum, kamar misalin Hassada da ke shafa da illata imani da gangar jikin mutum. To amma abin da nake nufi shi ne rashin gajiyawar wani shugaban Musulunci a tsarin Musulunci, ko kuma a wata ma’ana, “Gajiyar Da Gajiyar Kanta”, wanda ya kasance siffa ce ta Shahid Raisi da sahabbansa.

Shahadar Wannan Shahidi Tana Da Jarin Anfani Na Zamantakewa

Haka nan kuma yayin da yake ishara da falalar hidimar shahidi Raisi ga al'ummar Iran, Ayatullah Ramazani ya ce: Shahidi Raisi ya kasance mai fara'a, yana da dabi'a na sada zumunta, ya kware wajen gudanar da ayyukansa, sannan kuma ya dawwama a kan aikinsa. Don haka shahadar wannan shahidi tana da tasirin anfani ga zamantakewa, kuma muna fatan a zabe za a zabi wani mai yin hidima da yake da siffofi kamar ikhlasi da kusanci da al'umma don juyin juya halin Musulunci ya samu ci gaba da saduwa a cikin Babban birnin duniyar musulunci.

Da Yardar Allah Da Hikimar Allah Za A Maye Wannan Gibin

HUujjatul Islam Wal-Muslimin Dr. Abbasi, shugaban Jami'atu Al-Mustafa Al-Alamiya, a matsayin daya daga cikin masu jawabi na wannan taron, ya bayyana cewa shahadar masoyin shugaban kasa da sahabbansa a matsayin lamari mai radadi ga al'umma da Tsarin Musulunci mai tsarki da mai girma Jagoran juyin juya halin Musulunci, kuma ya ce: Amma duk da haka, mun yi imani da falalar Ubangiji da hikimarsa, wannan gibi da aka samu za’a maye gurbinsa, kuma wannan waki’a wani abu ne da aka saba da shi  irin kwatankwacinta sau da yawa a cikin abubuwan da suka faru na juyin juya halin Musulunci da suka gabata da fatan za mu shaida tabbatar da hakan a mataki na biyu na juyin juya halin Musulunci.

Shahidai Na Juyin Juya Halin Musulunci Ba Su Danfaru Da Wani Waje Kebantacce Ba Na Kasa

Yayin da yake godiya ga masu ruwa da tsaki wajen shirya wannan taron, ya ce: Al'ummar yankuna daban-daban na duniya suna mika gaisuwar ta'aziyya ga shugaban shahidan. Kuma halartar ku masoya daga sassa daban-daban na duniya shaida ce ga hakikar ce cewa wadannan shahidan juyin juya halin Musulunci ba su ke banta ga takamaiman wata ƙasa ba. Kamar yadda shima juyin juya halin Musulunci ci gaba ne na tafarkin annabawan Ubangiji, hakikar gaskiya ce ta gina sabuwar wayewar ruhi da ta mutumtaka da samar da abin koyi na rayuwar mutum da zamantakewa ga dukkan bil'adama.

Shugaban Jami’ar Al-Mustafa ya jaddada ga ruhiyar mutuntaka na shahidan, ya kuma bayyana cewa: Shahidai na hidima sun sadaukar da zaman lafiyarsu da nutsuwarsu da tausasawarsu ga kokarin yi wa al'umma hidima ta hanya mai haske, kuma ba su da wani hutu dare da rana a ranar aikin ko ranar hutu duka. Saboda Hakane kuma al'ummar Iran da sauran kasashen duniya ma'abota sanin girma sun nuna irin girmamawarsu ga wadannan shahidai masu daraja a cikin 'yan kwanakin nan.

Shahidan Hidima Na Daga Cikin Salihai Bayi

Shima Hujjatul Islam Wal-Muslimin Sheikh Abdullah Daqaq daya daga cikin malaman kasar Bahrain ya yi jawabi a wajen taron inda ya bayyana cewa shahidan hidima suna daga cikin masu gaskiya, ya kuma yi bayani a kan siffofin wannan halayya mai daraja ya ce: Siffa ta farko ita ce Ikhlasi a wurin Allah, mai irin wannan ba zai kasance da ruhin ma'aikaci ba sai dai zai zama ya dace da halayya ta Jihadi. Mutumin da yake da al'adar Jihadi bai san sa'o'in aiki ba. Duk wanda ya ga shahidai kamar Ayatullah Raisi, Dr. Amir Abdullahian, da Ayatullah Al-Hashem, ya ga al'adun Jihadi a cikinsu.

Wannan fitaccen malamin nan na Bahrain ya lissafta sifa ta biyu ta masu gaskiya da ruhin yi wa al’umma hidima ya kuma kara da cewa: Ya zo a cikin ruwaya cewa akwai halaye guda biyu wadanda babu wasu siffa a samansu, daya imani da Allah dayan kuma ita ce hidima ga mutane.

Sheikh Daqaq ya bayyana sifa ta uku ta Sadikai masu bi ga tafarkin majibinci lamari inda ya ce: wannan siffa ta fito fili a cikin Ayatullah Raisi da Dr. Amir Abdullahian.

A cikin wannan taron, baya ga gabatar da shirye-shirye daban-daban da suka hada da gungu-gungu na masu wake-wake na dalibai daga kasashe daban-daban, mawaka daga kasashe daban-daban sun yi ta karanta kasidu da yabo ga Ahlul Baiti (AS) da shahidan hidima.

A wani bangare na taron an karrama shahidan hidima tare da karrama iyalan shahidan.