Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Alhamis

30 Mayu 2024

21:47:34
1462371

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Daliban Jami’o’in Amurka: Ku Yanzu Kuna Tsaye A Bangaren Dai-Dai Na Tarihi

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei a cikin wata wasika da ya aike wa masu goyon bayan al'ummar Palastinu a jami'o'in kasar Amurka, yayin da yake nuna tausayawa da nuna goyon bayansa ga zanga-zangar kyamar sahyoniyawa da wadannan dalibai su ke yi, ya dauke su a matsayin wani bangare na gwagwarmaya. Kuma ya jaddada da yin hakan yana da tasiri wajen canza yanayi da makomar yankin yammacin Asiya.

 بسم الله الرّحمن الرّحیم

Ina rubuta wannan wasiƙar zuwa ga matasan da farkakken lamirinsu ya motsar su don kare yara da matan Gaza da ake zalunta.

Ya ku matasa dalibai da ke Amurka! Wannan shine sakon mu na tausayawa da kuma goyon bayanmu gareku. Yanzu kuna tsaye a bangaren daidai na tarihi - wanda ke gudana a hakin yanzu.

Yanzu kun kafa wani bangare na gwagwarmaya, kuma a karkashin yin matsin lamba ga zaluncin gwamnatinku - wacce ke ba da kariya ga gwamnatin sahyoniya ta mamaya da rashin tausayi - kun fara yin gwagwarmaya mai daraja.

Babban fagen gwagwarmaya da ke a wuri mai nisa ya kasance yana fito na fito a tsawon shekaru tare da hangen nesa da jin ku na yanzu. Manufar wannan gwagwarmaya ita ce dakatar da irin zaluncin da wata Cibiyar ta'addanci da rashin tausayi da ake kira "Sahyoniyawa" ta ke yi wa al'ummar Palastinu tun shekaru da suka gabata tare da jefa su cikin mawuyacin hali da azabtarwa bayan mamaye kasarsu. Kisan gillar da gwamnatin wariyar launin fata ta Sahayoniya ta ke yi a yau ci gaba ne na muguwar halayyar da suke yi ne a cikin shekarun da suka gabata.

Falasdinu kasa ce mai cin gashin kanta mai al'umma da ta kunshi Musulmai, Kirista da Yahudawa, kuma tana da dogon tarihi. Bayan yakin duniya, 'yan jari-hujjar cibiyar Sahayoniya tare da taimakon gwamnatin Burtaniya, sannu a hankali sun shigo da dubban 'yan ta'adda sanu a hankali cikin wannan kasa; Suka mamaye biranenta da ƙauyukanta; Dubun dubatar mutane ne aka kashe ko aka kore su zuwa kasashe makwabta; Sun kwace gidaje, kasuwanni, da gonaki daga hannunsu, suka kafa gwamnati mai suna Isra’ila a cikin kasar Falasdinun da suka kwace.

Babban mai goyan bayan wannan gwamnatin kwace, bayan taimakon farko na Birtaniya, ita ce gwamnatin Amurka, wadda ta ci gaba da goyon bayanta a siyasance da tattalin arziki da makamai ga wannan gwamnatin, har ma cikin sakaci da bazai yiwu a yafe ba ta bude mata hanyar kera makaman kare dangi da makaman nukiliya ta taimaka masa ta wannan hanya.

Tun daga rana ta farko gwamnatin sahyoniyawan ta yi amfani da manufar "karfin Karfe" a kan al'ummar Palastinu da ba su da kariya, tare da yin watsi da duk wata kima, ta dan Adam da ta addini, a kowa wace rana tana kara aikata zalunci da ta'addanci da danniya.

Gwamnatin Amurka da kawayenta ba su ma nuna adawa da wannan gwamnatin ta'addanci da zalunci da ke cigaba ba. Har yau, wasu kalaman gwamnatin Amurka dangane da munanan laifuka a Gaza sun fi a munafunce fiye da na gaske.

“Fagen gwagwagwarmaya” ya taso ne daga cikin wannan yanayi mai duhu da rashin tabbas wanda kuma da kafa gwamnatin “Jamhuriyar Musulunci” a Iran ta fadada ta tare da ba shi karfin gwiwa.

Shugabannin yahudawan sahyoniyanci na kasa da kasa, wanda ya zamo galibin kamfanonin yada labarai a Amurka da Turai nasu ne ko kuma suna karkashin tasirin kudadensu da cin hancinsu, sun gabatar da wannan gwagwarmaya ta mutuntaka da jajircewa a matsayin ta'addanci! Shin al'ummar da ta kare kanta a cikin kasarta daga laifukan sahyoniyawa 'yan mamaya 'yan ta'adda ne? Sannan shin taimakon ‘yan Adamtaka da ake baiwa wannan al'umma da karfafa makamanta ana iya daukarsa a matsayin ta'addanci?

Shugabannin mulkin mallaka na duniya ba sa jin tausayin ra'ayoyin ɗan adam. Suna goyon baya ga azzalumar gwamnatin ta'addanci ta Isra'ila, kuma suna kiran gwagwarmayar Palasdinawa da ke kare 'yancinta, tsaro da 'yancin kai, a matsayin "'yan ta'adda"!

Ina so in tabbatar muku cewa a yau al'amura sun canza. Wata makoma tana jiran yankin da ke da muhimmanci na yammacin Asiya. Lamiri da yawa a duniya suna kara farkawa kuma gaskiya tana bayyana. Kuma fagen gwagwarmaya yayi karfi kuma zai ƙara yin ƙarfi sosai. Tarihi kuma yana cikin canzawa.

Baya ga ku, daliban jami'o'i da dama a Amurka, jami'o'i da jama'ar wasu kasashe ma sun tashi tsaye. Suna masu goyon baya da tallafawa malaman jami'a gare ku dalibai wani abu ne mai mahimmanci kuma mai tasiri. Wannan zai iya zama ɗan kwantar da hankali idan akai la’akari da tsananin matakan ƴan sandan da gwamnati ke yi da kuma matsin lamba da suke yi. Ina kuma tausaya muku matasa kuma ina girmama matsayinku.

Koyarwar Alkur'ani gare mu Musulmi da dukkan mutanen duniya shi ne tsayawa kan tafarkin gaskiya فَاستَقِم کَما اُمِرت” (Suratul Hud, bangare na aya ta 112) kuma koyarwar Alkurani dangane da alakokin daa ke tsakanin mutane ita ce: “kada kuyi zalunci kuma kada ku bari a zalince ku”: (لا تَظلِمونَ وَ لا تُظلَمون) (Suratul Baqarah, aya ta 279) fagen gwagwarmaya da bin waɗannan umarni da ɗaruruwan makamantansu ta ke ci gaba kuma zata samu kaiwa ga nasara; Da yaddan Allah

Ina Mai Shawarartarku Da Ku San Alkur'ani.

Sayyid Ali Khamenei

5/3/1403

16/11/1445

25/5/2024