Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

20 Mayu 2024

11:14:42
1459752

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci: Raisi Madaukaki Bai san Gajiya Ba

Sakon Ta'aziyyar Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ga Shahadar Shugaban Kasar Iran Da Abokan Tafiyarsa

Jagora Ya Ayyana Zaman Makokin Kwana Biyar Domin Shahadar Shugaban Kasar Iran Da Abokan Tafiyarsa.

Ayatullah Khamenei, a cikin sakon da ya aike kan shahadar Hujjatul Islam Wal-Muslimeen Sayyid IBrahim Raeesi, shugaban kasar Iran da Dr. Amir Abdollahian, ministan harkokin wajen kasar, Hujjatul Islam Wal-Muslimeen Al-Hashim, wakilin jagora a gabashin Azarbaijan, Dr. Rahmati, gwamnan gabashin Azarbaijan, da sauran abokan tafiyarsu, ya bayyana alhininsa game da wannan hatsarin jirgin.

Sakon ta'aziyyar Jagoran juyin juya halin Musuluncin shi ne kamar haka;

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai 

Lalle Mu Daga Allah Mu Ke Kuma Gare Shi Muke Masu Komawa 

بسم الله الرّحمن الرّحیم

انا لله و انا الیه راجعون

Tare bakin ciki da takaicin na samu labarin shahadar Malami Mujahid, fitaccen shugaban kasa kuma mai kokari na mutane, Mai hidima ga Imam Ridha, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, Mai girma Hujjatul Islam Wal-Muslimeen Haj Sayyid Ibrahim Raisi da waɗanda suke tare da shi Allah Ya Jikansu da Rahmarsa.

Wannan mummunan lamari ya faru a lokacin ƙoƙarin yin hidima ga al'umma; Dukkanin wa'adin wannan ma'abocin daraja da kishin kai, a cikin kankanin wa'adin mulkin shugaban kasa da kuma kafin wannan lokaci, ya kare gaba daya a kokarin tsayawa wajen yi wa al'umma hidima da kasa da Musulunci.


Raisi madaukaki! bai san gajiyawa ba. A cikin wannan mummunan lamari al'ummar Iran sun rasa wani bawa mai gaskiya kuma mai kima. Ya fifita jin dadin jama’a da yardar Allah a kan komai, don haka bacin ransa ga wasu masu rashin godiya da izgilin na wasu masu mummunan nufi bai hana shi aiki dare da rana wajen inganta al’amura ba.

A cikin wannan lamari mai tsanani, akwai fitattun mutane irin su Hujjatul Islam Wal-Muslimeen Al Hashem, fitaccen limamin Juma'a na Tabriz, Amir Abdullahian, Mujahideen kuma ministan harkokin waje mai fafutuka, Malam Malik Rahmati, gwamnan juyin juya hali kuma mai tsoron Allah na Gabashin Azabaijan, da kuma tawagar jirgin da sauran sahabbai su ma sun shiga cikin rahamar Ubangiji.

Ina shelanta zaman makoki na kwanaki biyar tare da mika ta'aziyyata ga al'ummar Iran. Kamar yadda sashi na 131 na kundin tsarin mulkin kasar ya tanada, Mista Mokhbar ne ke rike da mukamin shugabancin bangaren zartarwa, kuma ya zama wajibi ya shirya tare da shugabannin majalisun dokoki da na shari'a domin zaben sabon shugaban kasa cikin kwanaki hamsin.

Daga karshe ina mika ta'aziyyata ga mai girma mahaifiyar Malam Raisi da mai dakinsa mai girma da sauran wadanda suka yi saura daga ɓangaren shugaban kasa da iyalan abokan tafiyarsa masu daraja, musamman mahaifin Majid, Malam Al Hashem, ina mai rokon samun Hakuri da yin n Ta'aziyya gare su da neman Rahamar Allah ga waɗanda suka rasu.

Sayyid Ali Khamenei

11/11/1445

31/02/1403

20/06/2024