Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

20 Mayu 2024

02:10:09
1459599

An Gano Wani Wuri Mai Zafi, Wanda Mai Yiwuwa Ne Wurin Da Helikwafta Ya Fado Ne + Bidiyo

Wasu majiyoyi da suka hada da kamfanin dillancin labaran Anatoliya na Turkiyya sun bayar da rahoton gano wani wuri mai zafi a yankin, wanda mai yiwuwa na wurin da jirgin mai saukar ungulun ne ya yi hadari.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Majiyoyin fili sun kuma ruwaito cewa, an tantance wuraren da jirgin mai saukar ungulu da ke dauke da shugaban kasar Iran ke ciki, kuma a halin yanzu ana kan hanyarsu ta zuwa inda aka tabbatar.

Bidiyon Gurin Da Ke Nuna Wani Waje Mai Zafi Da Jirgi Mara Matuki Ya Gano Ana Tunanin Anan Jirgin Ya Fado 

Kawo yanzu dai babu wani rahoto na ganin tarkacen jirgin mai saukar ungulu

Duk da isowar wasu tawagogin ceto zuwa wurin da jirgin saman Turkiyya maras matuki ya sanar, tare da share sararin samaniyar, har yanzu ba a samu labarin tarkacen jirgin da ke dauke da shugaban kasar ba.

Kamar yadda hasashen yanayi ya nuna, nan da sa'a mai zuwa za'a fara dusar kankara da ruwan sama a wurin da hatsarin ya afku, kuma a yanayin fadi za'a ga wurin zai kai mita 2-3.