Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

19 Mayu 2024

18:05:11
1459560

Jagoran juyin juya halin Musulunci: Wajibi Ne Kowa Da Ya Yi Addu'a Ga Domin Lafiyar Wannan Rukunin Bayin Allah

Jagoran juyin juya halin Musulunci: Wajibi Ne Kowa Da Ya Yi Addu'a Ga Domin Lafiyar Wannan Rukunin Bayin Allah

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: bayan Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana damuwarsa da wannan lamari mai tayar da hankali a yammacin yau da ya faru da mai girma shugaban kasar Iran da abokan tafiyarsa a wata ganawa da iyalan dakarun kare juyin juya halin Musulunci da aka gudanar a daren ranar maulidin Imam Riza (a.s.). Yana mai cewa:

Muna fatan Allah Madaukakin Sarki ya mayar da shugaban kasa mai daraja da daukaka da abokan tafiyarsa cikin al'umma. Kowa yayi addu'ar Allah ya baiwa wannan gungu na bayin Allah amincin lafiya. Al'ummar Iran kar su damu ba, ba za a samu cikas a ayyukan ci gaban kasa ba.