Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Asabar

18 Mayu 2024

18:44:53
1459316

Fiye Da Kashi Uku Na Ɗaliban Ingila Suna Ɗaukar Hamas A Matsayin Ƙungiyar Gwagwarmaya Ne

Jaridar Daily Mail ta Ingila: A wani bincike da sama da dalibai dubu daya suka halarta, kashi 40% na daliban manyan jami'o'i 24 a Ingila sun dauki harin da kungiyar Hamas (Operation Storm Al-Aqsa) ta kai wa gwamnatin sahyoniya a ranar 7 ga watan Oktoba, ba ta'addanci ba ne, wani nau'i ne na gwagwarmaya.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: sama da jami'o'in Ingila 20, sun kafa tantuna don bayyana goyon bayan Falasdinu, inda dalibai suke ta rera taken intifada da gwagwarmaya tare da bayyana goyon bayansu ga Hamas.