Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Jummaʼa

17 Mayu 2024

11:55:56
1459062

Yaman: Sojojin Yaman sun Harbo Jirgin Amurka Maras Matuki Karo Na Huɗu + Hotuna

Birgediya Janar Yahya Saree ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa a yau- Juma'a

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Jiya da yamma ne sojojin Yaman suka harbo wani jirgin yakin Amurka maras matuki kirar MQ9 a lokacin da yake gudanar da wani mummunan hari a sararin samaniyar lardin Marib.

Wannan jirgi maras matuki na dala miliyan 32, shi ne jirgi mara matuki na hudu da aka harbo a lokacin yakin "Nasarar Alkawari" da "Jihadi Mai Tsarki don Tallafawa Gaza".

Wannan jirgi mara matuki dai an harbo shi ne da makami mai linzami wanda ake harbawa daga kasa zuwa sama da kasar Yemen ta kera, kuma za a buga hotunansa nan ba da jimawa ba.