Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Jummaʼa

17 Mayu 2024

11:12:49
1459051

Iran: Shugaban Hukumar Agaji Da Kai; Wajibi Ne Mu Kasance Masu Godiya Dare Da Rana Ga Ni'imar Wilaya

Shugaban hukumar bayar da taimako da agaji ta Iran ya ce: Wajibi ne mu kasance masu godiya da Ni'imar Wilaya dare da rana. Wannan ba wai zance ne sakaka ba cewa kasancewar Imam ma'asumi wata ni'ima ce ga duniya, kuma kasancewarsa ni'ima ce.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Hujjatul-Islam Wal-Muslimeen Khamushi, Shugaban hukumar bayar da taimako da agaji ta Iran ya ce: Limamai Ma'asumai da malaman duniya suna haifar da da gwagwarmaya ta nuna adawa da zalunci da mulki, kuma suna adawa da girman kai. Malaman fiqihu sun kasance kagara ganuwa mai karfi ta addinin Musulunci, kamar irin katangar da ake kewaye garuruwa da ita a zamanin da, kuma a yau wannan ganuwar tana a ma'anar bada kariya da tsaronmu ga iyakokinmu. Bangaren al’adu, addini da Mazhaba da Aqidah su ne kan iyakarmu na asali.

Hujjatul-Islam wal-Muslimeen Khamushi ta hanyar yin tambaya kamar haka: Wane azzalumi ne ya fi Amurka da sahyoniya? Ya kara da cewa: Kungiyoyin Da'aash da Takfiriyya da sahyoniyawa abu guda ne. Wannan abin alfahari ne ga jagoranmu masoyinmu wanda ya mari bakunan sahyoniyawa da shi.

Ya kara da cewa: Manyan kasashen duniya sun so ruguza kasar Yemen, amma sun kasa. Akalla kasashe shida ne suka sha kashi a Yaman. Yanzu haka cikin saukin Mujahidai Yamanawa suna kaiwa tashoshin jiragen ruwan Isra'ila hari.

Shugaban hukumar bayar da taimako da agaji ta Iran ya ce: Wajibi ne mu kasance masu godiya da Ni'imar Wilaya dare da rana. Wannan ba wai zance ne sakaka ba cewa kasancewar Imam ma'asumi wata ni'ima ce ga duniya, kuma kasancewarsa ni'ima ce. 

Hujjatul-Islam Walmuslimeen Khamushi ya ce gaba dayan fagagen Shaidan sun hade a fage daya suna aiki tukuru: Idan da ace Wilayat wacce take a matsayin asalin igiya ba to da a yau babu abin da ya rage na Shi'a da Musulunci. Za mu yi amfani da reshen Wilaya kuma mu ci gaba da wannan tafarki har zuwa bayyanar shugaba har ya zamo mun mika wayewar ga Imam Zaman (A.S) da zai gamsu da ita.

........