Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Laraba

15 Mayu 2024

15:25:33
1458761

Afghanistan; Majalisar Malaman Shi'a Sun Yi Kira Ga Kungiyoyin Agaji Na Duniya Da Su Taimakawa Waɗanda Anbaliyar Ruwa Ta shafa A Baghlan + Hotuna

Majalisar Malaman Shi'a sun yi kira ga Kungiyoyin agaji da ofisoshin Taqlid da cewa yakamata suyi gaggawar taimakawa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Baghlan.

Dangane da bala'in ambaliya a Baghlan, wanda ya yi sanadin mutuwar daruruwan mutane, Majalisar malaman Shi'a ta Afganistan ta bukaci dukkanin muminai, cibiyoyin agaji da ofisoshin Marajio'in Taqlid da kuma shugabanni gwamnatin rikon kwarya da su taimaka wa wadanda lamarin ya shafa da dukkan hanya mai yiwuwa da wuri-wuri da kuma sauke nauyin da ayyukan Musulunci da na dan Adam da ya hau kansu.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: Majalisar malaman Shi’a ta kasar Afganistan, a matsayin martani ga mummunar ambaliyar ruwa da ta afku a birnin Baghlan, wanda ya yi sanadin mutuwar daruruwan mutane, ta roki dukkanin muminai, cibiyoyin bayar da agaji da kuma ofisoshin Marajio'in taqlid da gwamnatin kasar su yi gaggawar taimakon wadanda abun ya shafa da kuma gudanar da sauke nauyi da ayyukansu na Musulunci da na jin kai da ya hau kansu 

Majalisar malaman Shi'a ta kasar Afganistan ta mika ta'aziyyarta ga dukkan wadanda suka mutu da kuma iyalan wadanda suka rasu, tare da addu'ar Allah ya jikan wadanda suka rasu, ya kuma gafarta musu, ya kuma basu hakurin rashinsu tare fatan samun lafiya ga waɗanda su ji raunuka.


Cikakken bayanin Majalisar malaman Shi'a a Afganistan dangane da bala'o'in Anbaliyar ruwan da ya faru a kasar a baya-bayan nan shi ne kamar haka:

 بسم الله الرحمن الرحیم.

‏ عن النبي(ص ) : مَنْ أَصْبَحَ لاَ يَهْتَمُّ بِأُمُورِ اَلْمُسْلِمِينَ فَلَيْسَ مِنْهُمْ وَ مَنْ سَمِعَ رَجُلاً يُنَادِي يَا لَلْمُسْلِمِينَ فَلَمْ يُجِبْهُ فَلَيْسَ بِمُسْلِمٍ.

An karbo daga Annabi (SAW): Wanda ya wayi gari bai damu da al’amuran musulmi ba, ba ya cikin su, kuma wanda ya ji wani mutum yana kiran ya ku musulmi ku taimakeni bai amsa masa to shi ba musulmi ba ne.

Al'ummar musulmi da ma'abuta daraja na kasar Afganistan, wadanda suka sha wahala a baya-bayan nan; A cikin wadannan kwanakin bala'o'i, da suka hada da mummunar ambaliyar ruwa, da ta yi mummunar barna ga wadannan mutane. Musamman a lardin Baghlan, ya yi sanadin hasarar rayuka da barna ga jama'a; Rahotanni sun ce daruruwan mutane ne suka mutu tare da lalata dubban gidaje tare da duk wani kayan aiki da kayan masarufi, haka kuma ya lalata wasu dabbobin shanu da kananan dabbobi masu yawa.

Majalisar malaman Shi'a ta kasar Afganistan na mika ta'aziyyarta ga dukkanin iyalan wadanda suka rasu da kuma wadanda suka rasu, tare da yin addu'ar Allah ya jikan wadanda suka rasu, da kuma wadanda suka tsira da ransu ya ba da hakuri da lafiya. Saboda haka ga ofisoshin Marajio'in Taqlid, musamman ma gwamnatin rikon kwaryar Afghanistan da su gaggauta kai dauki ga wadanda abin ya shafa ta kowace hanya da ta dace kuma a kalla saboda haka a iya rage wa wadanda abin ya shafa wasu wahalhalu ta hakan kuma zai zama sun gudanar da ayyukansu na Musulunci da na yan Adamtaka.

Amincin Allah ya tabbata Agareku 

Majalisar Malamai ta Shi'a ta Afganistan


....................