Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Talata

14 Mayu 2024

19:49:25
1458544

A ganawarsa da mambobin kwamitin ilimi na taron duniya na Imam Rida (a.s) karo na biyar.

Jagoran juyin juya halin Musulunci: Daya Daga Cikin Manyan Nauyin Da Ke Wuyanmu Shi Ne Gabatar Da Imamai (As) Ga Duniya.

Yayin da yake karbar bakuncin wakilan kwamitin ilimi na taron Imam Rida (a.s) Jagoran juyin juya halin Musulunci ya tabbatar da cewa daya daga cikin manya-manyan nauyin da ya rataya a wuyanmu na 'yan Shi'a shi ne gabatar da Imaman mu (a.s) ga duniya.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya jaddada a ganawarsa da mambobin kwamitin ilimi na taron duniya na Imam Rida (a.s) karo na biyar cewa a nawa ra'ayi a matsayinmu na 'yan shi'a a matsayin al'umma 'yan shi'a daya daga cikin manyan ayyukanmu shi ne gabatar da imamai A's a duniya.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: – Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada a ganawarsa da mambobin kwamitin ilimi na taron duniya na Imam Rida (a.s) karo na biyar a matsayinmu na ’yan Shi’a, daya daga cikin manyan ayyukanmu shi ne mu sanarwa da duniya limamanmu As.

 Bayanin Ayatullah Khamenei a wannan taron ganawa shi ne kamar haka: Da farko dai kafa wannan kwamiti da wannan taro abu ne mai kyau matuka, domin mu - a cikin al'ummar Shi'a; Yanzu, kafin mu kai ga wasu, muna da nakasu da yawa a fagen ilimin sanin A'immah; Wani lokaci ana mai da hankali kan wani bangare da yawa sannan kuma a yi watsi da sauran bangarorin; Kuma a wasu lokuta ma ba a kula da wannan bangaren yadda ya dace, kuma sai a wadata a tsaya ga wadannan al’amura na zahiri da suke a bayyane kawai.

Ni a ra’ayina, mu ‘yan Shi’a a matsayinmu na al'ummar Shi’a, daya daga cikin manyan ayyukanmu shi ne gabatar da limamanmu ga duniya. Yanzu, wasu Imamai (amincin Allah ya tabbata a gare su) kamar Imam Husaini (a.s) da Amirul Muminin (a.s), an gabatar da su ne saboda wasu dalilai; sai ya zamo wasu sun yi rubuce-rubuce da fadi a kansu, kuma akwai wani nau’i na sanin su a qasar da ba ta ‘yan Shi’a ba, har ma da wadanda ba na Musulunci ba; Amma mafi yawan imamai (amincin Allah ya tabbata a gare su) ba a san su ba. Ba a san Imam Hasan Mujtaba da wannan girman kamar haka ba, Imam Musa bin Jaafar, Imam Hadi, Imam Jafar Sadik, duk da wannan manyan Asasi mai girma da aiki na ban mamaki da suka aikata, amma duka wadannan ba a san su ba a duniya. Koda an ce wani abu a kansu daga wadanda ba Shi’a ba – ba ‘yan Shi’a ba ne suka fada, to kaga abin da aka faadaa din ba na mazhaba ba ne – kuma dan kadan ne kuma mai iyaka. Yanzu, alal misali, wani marubucin sufanci ya ambaci sunan Imam Jafar Sadik a cikin sufaye, misali, ya yi magana game da shi a matsayinsa na sufi na rabin shafi ko kasa da haka; zaka Wannan [gabatarwa] iya karta ga iya wannan ne kawai babu sama da haka.


Ni a ganina ya kamata a yi la’akari da rayuwar imamai (amincin Allah ya tabbata a gare su) ta fuskoki uku: daya daga cikinsu shi ne yanayin ruhiyya na Ubangiji, wato tsarkakuwa; Bangaren tsarkin Imamai (amincin Allah ya tabbata a gare su); Ba za a iya rufe ido da wannan ba; Wannan ya kamata a yi magana a kansa amma a yi magana akan shi yadda ya kamata. Wani lokaci ana fadin kalmomi, ana bayar da ruwayoyi don karfafa wadannan sashen, [amma] kalmomin suna da rauni sosai. Wajibi ne mu bayyana yanayin matsayin sarauta da ruhiyya ta kujerar mulki na imamai A's; Wannan ba yana cikin abubuwan da muke so mu yi takiya ne akan su ba, misali ko mu yi kokarin boye su; A'a, dole ne mu bayyana wannan al'amari na Ruhiyya da sauratar imamai A's; Kamar yadda [muka fadi hakan game da Annabi sawa. Mas’alar barrantarsu, da batun alaƙarsu da Allah madaukaki, da alaƙarsu da mala’iku – ma'ana yadda suke– waliyyarsu a ma’anarta ta ruhiyya, wajibi mu fade ta; A wannan yanayin, kuma ya kamata a yi aiki mai karfi na ilimia wannan ɓangaren.

Bangare na biyu kuma shi ne bangaren hadisai da darussa na Wadannan hadisan- wadanda kuma ka ambata - a fagage daban-daban; A cikin abubuwan da suka shafi rayuwa, batutuwa daban-daban da mutane ke buƙata: ɗabi'a, zamantakewa, addini, hukunce-hukunce; lmamanmu suna da hadisai, suna da makaranta [wanda ya kamata a bayyana ta].

Wasu daga cikin wadannan bangarori, wadanda ba mu mai da hankali a kansu ba, suna da matsayi a duniya; Yanzu, alal misali, a ce batun kare dabbobi; Dubi irin bahasi da aka yi a cikin ruwayoyinmu daga limamai dangane da batun girmama dabbobi da kare dabbobi; Idan aka bayyana wannan ga duniya, aka san shi, to abu ne mai muhimmanci. Yanzu kayi duba ga hakan waye daga cikinmu yake tunanin wannan yanzu? Wanene a cikinmu yake neman tabbatar wannan batu? [ko maudu'in] mu'amalolin zamantakewa, jigogi ne da suka shafi kulla alaka da wadanda ba Shi'a ba da wadanda ba musulmi ba; Duk wadannan suna nan a cikin ruwayoyinmu a cikin wannan mahallin kamar yadda Alkur’ani mai girma ya ce: [Alal Misali]:

«لایَنهاکُمُ اللهُ عَنِ الَّذینَ لَم یُقاتِلوکُم فِی الدّین‌»

“Allah bai haneku kyakkyatatawa ga waɗanda ba su yake akan addini ba"

Dukkan wadannan suna daga koyarwar Imamai Ma'asumai Ya kamata a bayyana su kuma a yaɗa su.

 Duk yawan littattafai da mu ke da su; alal misali, Bihar al-Anwar [fiye da] juzu'in littattafai ɗari; Kuma akwai irin waɗannan littattafan da yawa...


 (Baitocin waka acikin Yaren Farisanci)...

Wannan ya kamata a nuna wa duniya a cikin harshen zamani na yau, a cikin harshen fasaha, tare da hanyoyin da suka dace. A yau, sadarwa a duniya ta zama mai sauƙi; Wato ka zauna a nan ka danna maballin ka shafe minti goma ya isa, a mafi nisa na duniya - Australia, Kanada, Amurka, a kowane wani wuri a duniya - duk wanda kake so zai ji ka. Wannan yana da matukar muhimmanci. A cikin wannan aikin, ya kamata a yi amfani da wannan hanya; Duk da haka, harshe yana da mahimmanci; Wane harshe kuke son bayyanawa? Wannan shi ne kashi na biyu na abin da ya kamata a bi don gabatar da limamai.


Kashi na uku kuma shi ne batun siyasa; Sashen siyasa sashe ne mai matukar muhimmanci. Wanda nayi bincike shekaru da dama na rayuwar A'immah cewa Me A'immah suke aikatawa kuma Me suke son aikatawa? Bangaren siyasa na A'immah bangare ne mai matukar muhimmanci amma menene manufar siyasar A'immah? Cewa Imam da dukkan wadancan matsayin da dukkan darajar Ubangiji da yake da shi da kuma kasancewar amanar Ubangiji tana hannunsa, ya zamo ya takaita kawai ga misali fadin wani adadi na hukunce-hukunce ko fadin wani adadi na kyawawan halaye da makamantansu ba, ina ganin cewa hakan ga mutum idan har yayi fahimtar daidai to zai zama ba abunda zai iya fahimta ba ne. Suna da manyan manufofi Babban burinsu shi ne samar da al'umma ta Musulunci; cewa kafa al'ummar musulmi ba zai yiwu ba sai an tabbatar da mulkin Musulunci; Don haka suke neman mulkin Musulunci. Wani muhimmin al’amari na Imamanci shi ne; Imamanci yana nufin shugabancin addini da duniya, shugabancin al'amari na jiki da ruhi. Kun gani, batunsa shi ne siyasa da tafiyar da kasa da tafiyar da gwamnati. Kuma dukkan limamai sun bi wannan; Wato ba tare da togiya ba, dukkan limamai sun bi wannan; Amma ta hanyoyi daban-daban, a cikin yanayi daban-daban, da salo daban-daban da manufofin acikin gajeren lokaci; [Amma] a manufar mai dogon lokaci kwara ɗaya ce.


Yanzu zan fadi wasu kalmomi game da Sayyidina Imam Riza (amincin Allah ya tabbata a gare shi). Yanzu, alal misali, a ce lokacin Imam Sadik (amincin Allah ya tabbata a gare shi); ansha zuwa wajensa ana tambayar Imam me ya sa ba kayi yunkuri ba; Muna da ruwaya da yawa kuma kuma gansu sun [tambayi] me ya sa ba kai yunkuri ba? Imam kuma yana bawa kowa hujja ko wata irin amsa daban. To, me ya sa suke yawan tambayar Imam me ya sa ba kayi yunkur ba? Dalilin haka kuwa an sanya cewa Imam zayyi yunkuri ne; kuma Shi'a sun san haka, wannan yana cikin abun Shi'a suka sallama da shi ne.

A lokacin da suka yi wa Imam Hasan Mujtaba (a.s) zanga-zangar cewa, menene dalilin da ya sa ya yi sulhu, daya daga cikin maganganun da aka sha nakalto daga Imam Mujtaba shi ne cewa ya ce:

«ما تَدری لَعَلَّهُ فِتنَةٌ لَکُم‌ وَ مَتاعٌ‌ اِلیٰ‌ حین‌»

 “Wa sanar da ku ce ta yiwu yin hakan fitina ne agareku da jin dadi na takaiccen lokaci" (5) wannan [Aiki] yana da lokaci, yana da wa'adi. me kuka sani Wato wannan alkawari ne fa. Kuma lokacin wannan alkawari ya zo a cikin ruwayar Imam; Ya zo a cikin hadisi cewa: Allah ya sanya haka a cikin shekaru saba’in. Imam Mujtaba ya fadi haka ne a shekara ta 40, 41, domin an sanya za'ai wannan yunkuri ne a shekara ta 70 kuma a kafa gwamnatin Musulunci. Allah ya kaddara a yi wannan aiki a wannan lokaci. Sannan yana cewa: 

«فَلَمّا قُتِلَ‌ الحُسَینُ‌ عَلَیهِ السَّلَامُ اِشتَدَّ غَضَبُ اللَهِ عَلَی اَهلِ الاَرضِ فَاَخَّرَه‌»

"Lokacin da aka kashe Imam Hussaini, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, fushin Allah ya tsananta a kan ga mutanen doron kasa"; Ya kamata a yi wannan [aiki] a shekara ta 70, [amma] saboda shahadar Imam Husaini As da kuma abubuwan da suke da alaka da wannan a zahiri, sai aka jinkirta wannan aikin. To, a tafsirin ruwaya, shi ne “fushin Allah a kan mutanen duniya”, amma mun san cewa wannan “fushin” da abin da ya haifar da shi, ya dace da wadannan abubuwa na zahiri da kuma sanadi na gama gari da dalilai; Abubuwan da suka saba da shi su ne, wanda kuma a wata ruwayar: Mutane sun yi ridda bayan Hussaini sai nau'i uku; “ Ridda” ba ya nufin sun kau da kai daga addini, wato bayan Imam Hussaini, ‘yan Shi’a sun yi shakku kan yadda suke tafiya; Wato ta yaya za ku iya tafiya da wannan yanayin? Sai dai mutum uku: Yahya bin Umm Tuwil [da wasu biyu]; Babu fiye da mutum uku da suka rage. Sayyidina Sadik yana cewa: “sannan sai mutane suka karu su kai yawa”, (7) shekaru talatin na aiki tukuru da Imam Sajjad ya yi, sannan da kokarin da Imam Baqir ya yi, sakamakon hakan ne mutane suka karu.

 To, a cikin [cigaban] wannan ruwayar da nake karantawa, Allah Madaukakin Sarki ya jinkirtar da gwamnatin da ya kamata ta faru a shekara ta 70 zuwa shekara ta 140; (8) Shekara ta 140 ita ce shekarar rayuwar Imam Sadik; kuma a [shekara] ta 148 ya rasu. An fadi wannan [nassi] kuma ana maimaita shi a cikin 'yan Shi'a, cikin kebantattun yan Shi'a. Sannan kuma tabbas Imam ya ambaci dalilin jinkirtawan daga baya a cikin wannan ruwayar, ta yadda jinkirin ya faru. Don haka, za ka ga - wannan a cikin ruwaya yazo - cewa Zurarah - wanda a yanzu yana cikin mafi kusanci; Zurarah yana Kufa; Kun san shi mutumin Kufa ne mazaunin Kufa ne – ya aika da sako zuwa ga Imam Sadik (a.s) ya rubuta wasika zuwa ga Imam Sadik (a.s) ya ce wani abokinmu daga cikin jama’armu, wato ‘yan Shi’a yana cikin matsalar bashi a nan. kuma gwamnati na son ta kama shi saboda bashin da ake bin sa. Wannan [mutumin] ya jima yana gudu; Ya gudu daga matarsa ​​da ɗansa ya gudu don kada su kama shi. [Zurarah ya rubuta:] Yanzu ina tambayar ku shin “wannan lamari” – “wannan lamarin hukumar” an maimaita shi a hadisai da dama; Wato batun gwamnati – idan “wannan al’amari” ya faru a cikin shekara daya ko biyu, sai a ce da wannan (mutumin) lamarin zai kasance ta kai ga ya faru, sai ku zo muyi aikin a warware matsalar; Amma idan ba a shirya ba, wannan [al'amari] ba a yi shi nan da shekara daya ko biyu ba, mu taru, mu tara kudi mu biyawa talakan nan bashi ya dawo gida ya zauna. Wannan ba wasa ba ne. Me ya sa Zurarah ya ba da yiwuwar hakan zai faru a cikin shekara ɗaya ko biyu?

Har ila yau, ya zo a wata ruwayar daga Zurarah, yana cewa: 

«و الله لا اری علی هذه الاعواد الّا جعفراً»

"Na rantse da Allah, babu wani da nake ganin ya dace da wannan mimbari sai Jafar" (10) "Awad" yana nufin mimbari, watau ginshikan mimbari; Ya ce, ni ban ga kowa ya dace da shi ba sai Jafar a kan ginshikan nan mimbarin nan. Yana nufin ya tabbata Imam zai zo ya zauna a kan mimbarin halifanci; Yana nufin cewa wannan [jinkirin] ya wanzu. Bayan haka:

«یَمحُوا اللَهُ ما یَشاءُ وَ یُثبِتُ‌ وَ عِندَهُ اُمُّ الکِتاب‌»؛

“Allah yana shafe abun da ya ke ya kuma tabbatar da abunda ya ke so a wajen shi ilimin dukkan littafi ya ke” haka Allah ya Kaddarar, amma abun da Allah ya hukunta ba kenan, wato abin da aka yanke faruwarsa ba ne, Saboda dalilai na musamman. Don haka limamai suna neman wannan lamari; saboda Wannan lamari ne mai matukar muhimmanci.

Yanzu za ku ga mene ne matsayin gudunmawar da Imam Rida (a.s) ya bayar a cikin wannan babin. Yanzu, ba shakka, ban tuna abin da ke cikin waccan jawabin na mai girma da ya yi ba; Kafin haka, a cikin shekarar farko, na aika da sako zuwa Mashhad kuma a cikin wannan sakon na yi nazari kan mas’alar karban Yariman cin Imam Rida. Bisa hakika na ce a gaskiya wannan fada ne tsakanin mai hankali da wayo kuma haziki Mamun da Imam Rida. Ma'amun da farko ya ce, zan ba da halifanci; da farko ba yarima ya ce; Ya ce, zan ba ka halifanci. Imam bai karba ba; ya nace sosai amma bai karba ba, Sannan ya ce yanzu tunda ba zaku karba ba, to ka [karbi] Yarima mai jiran gado. Menene dalilin da yasa Mamun ya aikata haka? Ni [a cikin wannan sakon] na ambaci dalilai hudu ko biyar ga Mamun cewa yana tunanin wadannan manufofin kuma yana neman samun wadannan abubuwa ne. Imam (a.s) ya karba; Na kuma ambaci dalilai biyar ko shida na yadda Imam ya yarda da abin da ya sa yayi haka da kuma mene ne fa'idar yin wannan aiki. Wani gagarumin yunkuri ne yakin basasa ruwan sanyi ne na ban mamaki, wato yakin siyasa a haƙiƙa, an fara shi tsakanin Imam da Ma'amun, acikin yaƙin, Imam ya murkushe Ma'amun. Wato da abin da ya yi ya durkufar da Ma’amun ne, Don haka tilas Ma’amun ya kashe Imam. Duk da ba haka ba ne da farko; Suna girmama [Imam] ne suna yin addu'a agareshi; suna daga cikin wadannan abubuwa da suke aikatawa. Yanzu a ciki na yi bayanin dalilin da ya sa Mamun ya yi waɗannan abubuwa da kuma dalilin da ya sa ya yi su da kuma abin da ya sa a gaba da kuma amfanin da yake da shi; A wancan lokacin, kamar ku, ku matasa masu jini ajika, alhamdu lillahi, mun kasance mun gunduri, mun kasance muna yin waxannan abubuwa; Yanzu da muka yi nisa gaba ɗaya daga waɗannan ma'anoni.

Don haka sai a tabbatar da bayanin wadannan bangarori guda uku na rayuwar Imam Rida (a.s) da sauran limamai. Aikin ku shine fara fitar da waɗannan sassa guda uku; Na biyu, a wanke su daga wuce gona da iri da kalmomin da ba su dace ba; Na uku, wannan na uku shi ne ya fi kowanne muhimmanci, tare da yin sa cikin yaren da ya dace, da harshen zamani, da harshen da wanda ba ‘yan Shi’a ba zasu fahimta har ma da Shi’a za su iya fahimta – domin tazarar wasu daga cikin matasanmu dags wadannan koyarwar bai gaza ba nisan dake ga wadanda ba Shi'a ba da wadanda ba musulmi ba ba su da basu da labarin hakan - don ku yi bayani su. A ra’ayina, idan aka yi wannan aiki, ba za a sami yin wani taro da jawabai da makamantansu ba. Ma'ana ina nufin cewa wata fa'ida ta zahiri za ta auku.

 والسّلام علیکم و رحمة‌الله و برکاته


 ................................