Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Talata

7 Mayu 2024

19:34:13
1456948

A Taron Ganawa Da Malamai Masu Tabligi Da limaman Juma'a Na Indiya;

Ayatullah Ramezani: Ya kamata Limaman Juma'a Su Tsaya Tsayin Daka Wajen Yaƙi Da Bidi'o'i, Shubuhohi Da Sauka Daga Addini.

Babban sakataren Majalisar Ahlul Baiti (A.S) ya bayyana cewa: Limaman Juma a birnin da yake aiki ya kamata ya gina ma'aikata da horar da masana ta hanyar zakulo mutane masu nagarta da aiki da kuzari da gabatar musu da hukunce hukuncen addini.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA - ya habarta maku cewa: tawagar masu tabligi da limaman Juma'a na kasar Indiya sun gana da babban sakataren majalisar duniya ta Ahlul-Bait (AS) da yammacin jiya Litinin 6 ga watan Mayu 2024

A cikin wannan taron ganawa, Ayatullah Riza Ramezani ya yaba da ayyukan limaman Juma'a na Indiya, inda ya ce: Na kasance limamin Juma'a tsawon shekaru 17 Shekaru 4 a Karaj da shekaru 13 a Austria da Jamus.

Ya ce dangane da ayyukan limamin Juma'a: Ayyukan limamin Juma’a sun bambanta da na limamin jam’i. Limamin jama'a yana kula ne da masallaci kwara daya, kuma masallacin ya zamo shi ne kagara wajen bayanin ilimi. Muhimmin aikin limamin jama'a shi ne kiyaye addinin mutane. Wajibi ne limamin jama’a ya san addini daidai kuma ya yada shi yadda ya kamata, karfafa ilimin addini da imani da addini yana daga cikin muhimman ayyukan limamin jam’i, domin mutane masu addini; Su san zamowa mai addini da sanin addini kansa.

Farfesan Malamin Hauza ya ci gaba da bayyana cewa Limamin Juma’a yana da ayyuka mafi muhimmanci a cikin al’umma: Limamin Juma’a na iya aiki a cikin da’ira mai fadi, don haka aikinsa na farko shi ne daidaita ayyukan addini. A daya bangaren kuma, samun damar da ake bukata na amsa tambayoyi da Shubuhohi da hada karfi da karfe na hujjoji.

Ya ce dangane da wajibcin bayanin koyarwar addini da limaman Juma’a ke yi: “Kada mu kebe wajen bayanin koyarwar addini, domin koyarwar tana da alaka da juna, kuma akwai alaka ta kut-da-kut a tsakanin bangarori daban-daban na ilimin addini, don haka limamin Juma’a wanda ya ke bincike da bayani akan addini yakamata yayi dubi zuwa ga tarin mas'alolin addini.

Ayatullah Ramezani ya bayyana wajibcin amsa Shubuhohin addini a matsayin daya daga cikin sauran hadafofin limaman Juma'a sannan ya ci gaba da cewa: A yau wasu mutane suna cakude gaskiya da karya suna yada shakku da neman raunana akidar mutane. Shakku ya kasance a kowane zamani, amma zamanin yau shi ne lokacin tsatstsan haifar da shakku, kuma shakku kan hauhawa a kowace rana.

Ya kara da cewa: Daga cikin shakkun da yake tasowa akwai batun sauya Shari'a da sabbin ayyuka. Misali, sun ce za ka iya samun madadin azumi ko sallah. Ta hanyar yin wannan magana, suna ƙoƙarin ragewa da rufe shari'ar. Har ma suna maye gurbin harshen larabci da harshen gida a cikin sallah. A yau, shakku yana kara yawa ta hanyar sararin samaniya kafafen sada zumunci, kuma a wannan fili, limaman Juma'a yana da alhakin samar da amsa ga shakku da Shubuhohi.

Babban sakataren majalisar duniya ta Ahlul-Baiti (AS) ya ambaci wani misali na zarge-zargen da ake yi wa Musulunci a yanar gizo inda ya ce: Wasu mutane da kyakykyawan tawili da suke da'awar cewa Musulunci addinin rahama ne, yayin da ya zamo addinin rahama kenan baya gwagwarmaya da adawa da zalunci da azzalumai. Dangane da haka muna da ayoyi da ruwayoyi da ke nuni da cewa lallai Musulunci mai rahama dole ya zamo yana hade da gwagwarmaya da tinkarar azzalumai. Marigayi Imam Khumaini (r.a) ya ce dangane da ruwayoyin da suke nuni da rashin halascin yin wani yunkuri kafin bayyanar Imam Mahadi A's; wadanda ba su da wani abin yi suna malalata suna amfani da wadannan hadisai wajen rufe bakin wajen hana tunkarar azzalumi. Suna ganin cewa dole ne zalunci ya yadu ako ina domin Imam (A.S) ya bayyana! Don haka suke cewa bai kamata malamai su shiga fagen siyasa ba, alhali a muna karantawa a Ziyaratul Jami'ah Kabirah cewa Imamai Alaihimus salam sune “Sasatul Ibad” wato jagorori shugabanin al’umma.

Ya ci gaba da cewa: Wajibi ne limamin Juma'a ya tsaya kyam wajen yakar bidi'o'i da Shubuhohi da karkatacewar hanya kuma ya kasance mai kare addini da tsarkake addini. A daya bangaren kuma wajibi ne limamin Juma’a ya kasance da jajircewa da ‘yanci wajen bayyana gaskiyar addini.

Farfesan na manyan jami’o’i ya gabatar da aiki gina tarbiyya a matsayin daya daga cikin ayyukan limamin Juma’a inda ya bayyana cewa: Limamin Juma’a a birnin da yake aiki ya kamata ya gina ma’aikata da horar da masana ta hanyar zakulo mutane masu nagarta, masu aiki da kuzari da kuma gabatar da ayyukan addini zuwa gare su.

Da yake bayyana cewa gina fasaha na da matukar muhimmanci ga limaman Juma'a, ya kara da cewa: Domin tattaunawa da fasahar sadarwa, ya kamata a gudanar da tarukan horaswa na musamman da masu halartar taron za su fahimci addinan dan adam da kuma koyarwar Musulunci guda daya. A kasashen yamma, wasu fastoci sun saba da harsuna hudu ko biyar, amma abin takaici muna baya wajen sanin harsunan duniya.

Babban shugaban majalisar Ahlul Baiti (AS) ya yi ishara da cewa Imam Juma'a ya kamata ya gabatar da addinin Musulunci ta hanyar da ta dace, sannan ya kara da cewa: Musuluncin Ahlul Baiti Musuluncin ne wanda yake da waje da ciki, da yake dauke da sassa na daidaikun mutane da zamantakewa a cikinsa. Haka nan, a cikin Musuluncin Ahlul-Baiti AS Yunkuri da sufanci suna a hade ne ba kawai yunkuri ne ko sufanci ba.

Ya jaddada cewa: Allah ya damka addini ga limaman Juma’a saboda haka ya kamata Limamin Juma'a ya kula da duniyar Musulunci, kuma dalilin da ya sa ake son karanta surorin Juma'a da Munafukai a Sallar Juma'a shi ne, Suratul Munafikai tana da alaka da sanin makiya. Don sanin mutanen da suke son raunana Musulunci.

A karshe Ayatullah Ramezani ya ce: Limamin Juma'a yana kiran masu ibada zuwa ga taqawa ta kashin kai da ta siyasa da zamantakewa, don haka limamin Juma'a yana da wasu ayyuka masu muhimmanci. Don Allah zai ba wa wadanda suka kiyaye addini a matsayin amana kulawa ta musamman.