Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Jummaʼa

3 Mayu 2024

12:56:00
1455888

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci A Ganawarsa Da Dubban Malamai Makarantun Iran:

Daidaita Dangantaka Da Isra’ila Ba Zai Magance Matsalar Ba; Dole Ne Falasdinu Ta Koma Ga Ma’abotanta Na Asali / Al'ummai Za Su Afkawa Gwamnatoci Masu Daidaitawa Da Isra’ila

Ayatullah Khamenei ya bayyana mafita guda daya tilo kan batun Palastinu da Iran ta gabatar, wato mayar da Palastinu zuwa ga masu ita na asali da suka hada da musulmi, kirista da yahudawa, sannan ya jaddada cewa: ba za a warware matsalar yammacin Asiya ba har sai an mayar da Falasdinu ga masu ita. Kuma ko da zasu iya kokarin ganin har zuwa shekaru ashirin ko talatin gwamnatin Sahayoniya ta ci gaba da rayuwa - wanda in Allah ya yarda ba za su iya ba - wannan lamari ba zai warware ba.

Kamfanin dillancin labaran na kasa da kasa na Ahlul-Bait (A.S) ya kawo maku rahoton cewa: a ranar Malamai ta duniya, dubban manyan malamai da kananan malamai na kasar Iran gaba daya sun gana da jagoran juyin juya halin musulunci, inda Jagoran juyin juya halin Musuluncin yayi magana cewa girmama malamai da masana a fadin kasar nan wajibi ne akan daidaikun al'umma. Tare da yin nuni da cewa koyar da ilimi yana da mahimmanci kuma yana da tasiri ba za a iya kwatanta shi da kowane tsarin ba, ya kara da cewa: tsara gina matasa da sabon tsatso da kuma samar da shauki da fata a gare su, ci gaba da gudanar da canji, kayan aiki na jiki da kayan aikin daba na jiki ga malamai, bada tallafi ga cibiyoyin horar da malamai, ƙarfafa shugabanni masu kula ilimi da masu gina makwafai a cikin al'ummar malamai, su ne mafi mahimmancin batutuwan aikin koyarwa.

Har ila yau Ayatullah Khamenei ya bayyana fadadar yadda ake gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga al'ummar Palastinu a Amurka da sauran kasashen duniya a matsayin wata alama ta ci gaba da bai wa al'ummar Gaza fifiko a ra'ayin al'ummar duniya tare da jaddada cewa: laifuffukan gwamnatin sahyoniyawa tare da hadin kan Amurka,  halaccin matsayin gwamnatin Iran da kuma al'ummar kasar wajen kin amincewa da gwamnatin mamaya, ya tabbatar da kyama ga Amurka, kuma kowa da kowa ya sani cewa, babu wata hanyar warware matsalar Palastinu, face mayar da wannan kasa ga ma'abotanta musulmi, yahudawa da kiristoci, kuma kulla alaka da gwamnatin sahyoniya da daidaita al'amura ba za su warware matsalar ba.

Da yake taya daukacin al’ummar malamai murnar zagayowar ranar malamai a matsayinsu na masu tarbiyyar nagarta da kuma gina makomar kasa, ya ce: maida hankalidaa girmamawar da kowa da kowa yak e yi ga malamai zai kara jawo sha’awa ga wannan aiki mai daraja, ya kuma daga darajar al’ummar malamai, a karshen lamarin kuma zai yi snadin daukaka da ci bagan kasa, kuma ya zama dole kafafen yada labarai da masu dandalin jama'a su tashi tsaye wajen bayyana matsayin malami da wajabcin girmama shi.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya lissafa dalilan da suka haifar da bambancin muhimmancin ilimi da horarwa ga sauran cibiyoyi yana mai cewa: dukkanin cibiyoyi suna amfani da albarkatun dan adam ne, amma ilimi da horarwa suke samar da albarkatun mutane ne.

Ayatullah Khamenei ya dauki malamai masu himma a matsayin masu gina al'ummar samari da sabon tsatso yana mai cewa: Duk wata magana ko halayya ko daukar matsayi kai har ma koda isharar malamai suna da tasiri a kan gina sabbin tsatso.