Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Talata

7 Faburairu 2023

03:41:00
1344264

Rufe Mu'utamar Din Muballigun Wanda Akayi A Kano Da Shekh Ibrahim Yakub Alzakzky (H) Ya Rufe

SHEKH IBRAHIM ELZAKZAKY (H): BA ANA YIN TABLIG NE A MATSAYIN AIKI NA NEMAN ABINCI BA

Sheikh Ibraheem Zakzaky jiya a jawabinsa na rufe taron Tablig da aka yi a Jami'atul Mustapha Kano.

Kamfanin dillanci labarai na Ahlul Bayt (As) ABNA ya kawo maku rahoton taron mu'utamar da aka gudanar na Masu Tabligi A Najeriya Jihar Kano wanda ya gudana a Madrastut Darul Thaqalain.Jami'atul Mustapha Kano.

"Dai-dai wannan lokacin duk wanda yake Tabligi kaman yana isar da saƙon Sahibul asri wazzaman ne ga mutane kafin bayyanarsa, saboda haka ƙaton aiki ne (Babban aiki ne) kuma aiki ne wajibi, kuma ana yin shi ne don Allah. Nasan mutane da yawa sukan damu da akan me zasu rayu, na'am ɗan Adam zai rayu yana da buƙata kan abubuwan rayuwa na yau da kullum (Abincinsa, suturansa, wurin kwanansa, abin hawansa da lafiyan jikinsa da sauran walwalarsa da sauransu amma basu ne hadafi ba waɗannan suna bi ne".


 "In dai kai kasa aikin isar da saƙo ne aikin ka to wadannan abubuwan zasu biyo. Ba ana yin Tabligi ne a matsayin aiki na neman abinci ba, ana yin Tabligi ne saboda Allah, wannan kuma muhimmin abu ne in kana Tabligin ka kayi shi saboda Allah, kana isar da saƙon Sahibul asri wazzaman ne wa Al'umma. Wannan isar da saƙon ya haɗa da karantar da mutane wanda shine muhimmi (muhimmin al'amari) wanda za a karantar da mutane tun daga yara har zuwa manya akwai yara ƙanana, akwai 'yan Iftida'iyya akwai 'yan Sanawiyya akwai kuma ajin manya. Aji yana da muhimmanci a zauna a karantar da mutane Addini, a karantar da mutane Aƙa'id a sanar dasu Ahkam, a karantar dasu Sirah a karantar dasu Aklaƙ, wannan a ajin karatu ya kamata a yi ba a bayyane ba, ba a gidan rediyo ba ko a gidan Talabijin ba".


 Malam (H) ya ƙara da bayyana cewa: "Sai kuma isar da saƙo na Amaa na kowa da kowa kaman wanda zamu ce masa kamar muce wa'azi wanda shi kuma za a iya yi ko a masallatai wanda za a tara mutane a yi magana dasu a masallatai ko lokacin Juma'a ne kafin ayi sallar juma'a ko bayan an yi sallar juma'a ko kuma a waɗansu munasabobi...". "....Sannan kuma na ambaci rediyo da talabijin to shima wannan, yanzu ma muna da hanyan da muke ce mishi hanyar sada zumunta wanda yake mutum shi da kansa zai zauna yayi magana yayi bayani dan mutane su amfana dashi.