Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Asabar

4 Faburairu 2023

07:07:16
1343408

A yayin bikin Goman Alfajr jagoran juyin juya halin Musulunci ya ziyarci hubbaren wanda ya assasa juyin juya halin Musulunci.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya isa hubbaren wanda ya assasa juyin juya halin Musulunci Imam Khumaini (R.A) tare da gabatar da gaisuwar ta'aziyya ga zagayowar alfijir na dawowarsa kasar Iran.

Kamfanin dillancin labarai na Ahle Bait (AS) Abna ya bada rahoton cewa: Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamene'i kamar kowace shekara ya ziyarci hubbaren jagoran juyin juya halin Musulunci Imam Khumaini (R.A) a safiyar talata data gabata a daidai lokacin da cika shekaru 44 da juyin juya halin Musulunci, suka cika, inda ya gabatar da addu'o'i. a can ya karanta Alkur'ani mai girma tare da girmama shi bisa irin nasarorin da ya samu da ba su misaltuwa a tarihi.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kuma halarci hubbaren Imam Khumaini (RA) da shahidan juyin ya kuma karanta Fatiha da yi masu Adduah Daga nan kuma ya je kaburburan shahidan manya na Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ayatullah Beheshti da shugaban kasar shahidan kuma firaministan kasar Iran Muhammad Ali Raja'i da Jawad Bahnar da kuma sauran shahidan juyin tare da yi masu addu'a daukaka darajar shahidai.


Wanda a ranar Laraba 1 ga watan Fabrairu ne aka fara fara bikin kwanaki 10 na cika shekaru 44 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci na Iran "Ashr Fajr".


Shekaru arba'in da hudu da suka gabata a ranar 1 ga watan Fabrairu ne wanda ya kafa jamhuriyar Musulunci ta Iran Imam Khumaini (R.A) ya dawo Iran bayan shafe shekaru goma sha biyar yana gudun hijira kuma al'ummar kasar suka tarbe shi. Kwanaki goma kacal bayan dawowar Imam Khumaini (RA) babban juyin juya halin Musulunci na Iran ya samu nasara.


  A kan haka ne a kowace shekara a cikin wadannan kwanaki a kasar Iran, ana gudanar da bukukuwan cika kwanaki goma na zagayowar ranar juyin juya halin Musulunci da sunan "Dahei Fajr" a cikin gagarumin tsari.


A halin da ake ciki kuma a safiyar ranar Dahei fajr wato Laraba aka fitar da muzaharar masu tuka babura daga filin jirgin sama na Mehrabad na Tehran zuwa Behesht Zahra kuma anyi ta ruwan furanni a wannan hanya.