Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Jummaʼa

27 Janairu 2023

11:17:40
1341321

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci: Makarantu, Jami'o'i, Kafar Yada Labarai Suda Wa Sima Sune Asalin Wadanda Ake Magana Da Su A Nan «اقیموا الصلاة».

Sakon Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Zuwa Babban Taron Sallar Kasa Na 29

Nassin sakon jagoran juyin shine kamar haka;


بسم الله الرّحمن الرّحیم


والحمدلله رب العالمین و صلی الله علی محمد و آله الطاهرین سیما بقیةالله فی‌العالمین ارواحنا فداه


Gudanar da wannan taro mai albarka bayan jinkiri na shekaru biyu abin farin ciki ne kuma in sha Allahu zai haifar da Albarka ne. 


Duk wani kokari na hankali da aiki na nuna kimar Sallah da girmama wannan aiki mai albarka wani abu ne da zai haskaka zukatan mutane da Karfafa yanayin rayuwarsu.


Zikirin Allah wacce sallah ita ce cikakkiyar bayyanarsa, tana ‘yantar da zuciya da ruhi da raya al’umma. Alamomi masu mahimmanci a cikin al'umma mai farin ciki da nasara, kamar abokantaka, gafara, kyautatawa, tausayi, tausayawa, taimako, kyautatawa, da makamantansu, albarkar Sallah suna ƙarfafawa. Sahun sallar jam'i suna haifar da Sahun zamantakewa masu alaƙa da juna Cibiyar Karfafa yanayi da kishin masallatai tana kara habaka cibiyoyin hadin gwiwa a fagen zamantakewa. Sallah idan aka yi ta da jin kasancewar Allah, tana haskaka dukkan fagagen rayuwa da kyautata duniya da lahira ga mutum da al’umma.


Mai sallah – kowaye kuma a ko’ina yake – ya amfana da sallah gwargwadon karfinsa, amma kafin nan, matasa sun fi kowa; Amfaninsu gareta bisa la'akari kulawa da tawali'u da kushi'i wanda dole da su ake yinta. Tana kara tasiri cikin Zuciyar samari da Matasa domin kaiwa fa samun rabo “Falah” da kiran sallah ya yi umarni da a gaggauta.


Iyaye maza da iyaye mata malamai da malaman Jami'ah masu ba da shawara da jagorori, su tuna da wannan gaskiyar a cikin alakar da ke tsakanin sallah da matasa kuma su gane aikin da ke wuyansu.


Makarantu, jami'o'i, musamman jami'ar Farhangian, kafar yada labarai Sida Wa Sima da sauran cibiyoyin al'adu, suna daga cikin manyan da ake magana da su anan " «اقیموا الصلاة».


Ina rokon Allah Madaukakin Sarki Ya ba kowa nasara.


Sayyid Ali Khamenei

  January 25, 2023