Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Jummaʼa

27 Janairu 2023

09:58:28
1341312

"Sallah waraka ce, annashuwa da shiryarwa ga dukkan mutane..."

Sayyid Dokta Raisi: Batanci Ga Alkur’ani da addinan Allah abu ne mai muni, abin kyama da kuma abun Allah wadai.

Yayin da yake yin Allah wadai da cin mutuncin Alkur'ani mai girma da ake yi a kasashen Turai da suke ikirarin cewa su ne madogaran 'yanci, shugaban ya jaddada cewa: Masu wulakanci ga kur'ani mai tsarki da fiyayyen halitta Annabi (SAW) su sani cewa wadanda suke wulakanta kur'ani mai tsarki sun ci mutuncin dukan addinan Ibrahim As da ɗan adam.

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (A.S) Abna- ya nakalto maku cewa Hujjatul-Islam wal-Muslimin, Dr. Sayyid Ibrahim Raisi a safiyar Alhamis data gabata a wajen taron Sallah a kasar karo na 29, ya mika godiyarsa ga Jagoran juyin juya halin Musulunci a kasar cikin dogon bayanansa da sakonsa mai fadakarwa ga taron addu'ain da jinjinawarsa ga kokari da kuma bayanan Hujjatul-Islam wal-Muslimin Qaraati a cikin wannan yake cewa: Sallah ita ce mafi kololuwar bayyanar da kyawawan halaye da ayyuka na kwarai ga bawa da kuma mai nema.

Shugaban ya bayyana cewa sallah tana da matukar tasiri wajen tunani da kyawawan halaye da kyawawan dabi’u da kuma ayyukan mai neman shiriya, sannan ya kara da cewa: “Watakila babu wata baiwar da Allah Ya yi wa dan’adam da ya kai Sallah wajen gina mutum da kuma al’umma. , kuma wannan shi ne nasiha da umurnin dukkan annabawan Allah Ta'ala dangane da sallah ce.


Dakta Raisi ya bayyana da kuma fayyace hukunce-hukunce da ladubban muhimman abubuwan da ke cikin sallah inda ya cigaba da cewa: hukunce-hukunce, abubuwan da ake bukata da sharuddan sallah da abin da ya shafi hukunce-hukunce da sharuddan sallah suna da matukar muhimmanci, amma idan mutum ya hadu da sirri na sallah, ruhinsa ya kan zama maɗaukaki, kuma idan sallar mutum ta ƙaru, wannan mai yin sallah din Shina yana ƙaruwa da sallarsa.


Shugaban ya bayyana cewa, albarkacin nasarar juyin juya halin Musulunci, tsari da nasihar dukkan annabawa da kuma nasiha ga Salloli da kuma al'ummar da suke yin sallah sun samu kyakkyawar kulawa, sannan ya ce: Ya kamata mu yaba da duk kokarin da aka yi a wannan lokaci na biyawa kula da sallah, amma duk da yawan abubuwan da aka yi, mun yi nisa da abin da ya kamata mu kasance.


Shugaban ya bayyana cewa kula da Sallah a yau shi ne mabudin samun 'yancin kai, 'yanci da kuma tabbatar da tsarin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, yana mai cewa: Hare-haren da ake kai wa mutanen da suke yin sallah na nuni da cewa salla ita ce babbar al'amari a kasar.


Dr. Raisi ya yi nuni da cewa: Bayar da sallah da kula da ladubban sallar al'ummar mutanen kasarmu sun kare mu daga fitina da makirci tun farkon nasarar juyin juya halin Musulunci.


Yayin da yake yin Allah wadai da cin mutuncin Alkur'ani mai girma da ake yi a kasashen Turai da ke ikirarin cewa su ne madogaran 'yanci. shugaban ya jaddada cewa: Masu cin mutuncin kur'ani mai tsarki da fiyayyen halitta Annabi (SAW) su sani cewa su na su masu bata kur'ani mai tsarkin sun ci mutuncin dukan addinan Ibrahim As da Yan adam.


Raisi ya kara da cewa: Wannan mummunan abu da kuma irin wannan lamari ana yin su ne da sunan 'yancin fadin albarkacin baki, wanda a zahiri shi ne mafi muni na cin fuska ga bil'adama. 


A duk fadin duniya babu wanda ya yarda da wannan yunkuri domin yaki da ‘yancin fadin albarkacin baki da kuma toshe ‘yancin fadin albarkacin baki a cikin al’ummar dan Adam. Batanci ga Alkur'ani da addinan Ubangiji abu ne mai banƙyama, da abin ƙi.


Dakta Raisi ya bayyana cewa, idan muna so mu gabatar da jerin laifukan da Turawa suka aikata a yau, za a gabatar da dogon tuhume-tuhume a kansu, ya kuma yi karin haske da cewa: Turawa da ke da’awar kare hakkin bil’adama, kamata a dora su kan teburin tuhuma don su bada amsar ga ra’ayin jama’a da musulmi.


A wani bangare na jawabin nasa, yayin da yake ishara da sakon da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya aikewa taron Sallar na kasar karo na 29, shugaban ya ce: A yayin gudanar da taron koli na kasa baki daya, Jagoran ya fitar da sakwanni 29 da wanda wadannan sakonni su ne fitilar haske ga Ma'aikata, shugabanni, masana al'adu da kuma masana zamantakewa ne.

Ya kara da cewa: Wajibi ne ma'aikatan Gudanar da sallah, malamai, malaman Jamiah da dalibai da matasa su dauki matakan da suka dace don cika burin jagoran juyin juya halin Musulunci a fagen Sallah.


Yayin da yake jaddada wajibcin gudanar da bincike a fagen Salloli, shugaban ya bayyana cewa: gwamnati tana ganin cewa wajibi ne ta bin diddigi da kuma cika shawarwarin da jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayar a fagen gabatar da salloli da kuma samar da salon rayuwa ta hanyar Sallah ga kowa da kowa.


Dr. Raisi ya kara da cewa: Wadanda suke taka rawa a fagen sallah a kasar, su ne masu saurare na musamman na sakon da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya aikewa majalisar dokokin kasar karo na 29, kuma mu aiwatar da wadannan umarni a cikin kasar, kuma Wajen aiwatar da wadannan umarni dole ne a yi ƙoƙarin yin salloli a cikin ƙungiyoyi da kuma a kowane wuri.


Shugaban ya ce: "Sallah waraka ce, annashuwa da shiryarwa ga dukkan mutane, kuma tana fitar da al'umma daga cikin wahalhalu da kuma samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali."


Da yake cewa sallah, zakka, umarni da kyakkyawa da hani da mummuna su ne tushe guda 4 na addinin Musulunci, Dakta Raisi ya yi nuni da cewa ruhin sallah ya kamata ya kasance a bayyane a dukkan bangarori na rayuwar dan'adam, musamman a tsarin gudanarwa, siyasa da tattalin arzikin kasa.


Shugaban ya bayyana cewa mai sallah yana da tasiri da yawa a cikin zamantakewa baya ga tasirin mutum na kan kan shi, inda ya ce: “Masu yin sallah na gaskiya ba mutane ba ne masu yin kasa agwiwa, cin hanci da rashawa, liyafa, da kuma rashin kyakkyawar alaka ta shugabanci ba.


Dakta Raisi ya yi nuni da cewa daya daga cikin hanyoyin da dabarun yada Fadakarwa don jawo hankalin mutane shi ne yadda jami'ai suke aiki daidai, kuma ya ce: Ma'aikata a kowane mataki su san cewa Sallah fa ita ce mafi kyawun wajen isar da halayen mu'amalarsu, Gaskiya cikin magana, aiki daidai, alakarsu tare da mutane da kuma tabbatar mutane duka ya samo asali ne daga yin sallah.


Da yake jaddada cewa umarni da kyakkyawa da hani da mummuna na da matukar tasiri wajen gyara al'umma, ya kuma yi karin haske da cewa: Ina gaya wa dukkan abokaina da Ma'aikata da su kula da ruhin sallah da kasancewar zuciya a cikin Yin Sallah yana da matukar muhimmanci a gare su. Haka kuma ministoci da gwamnoni da dukkan jami’ai su kula da gudanar da Salloli a ofisoshinsu.


A wani bangare na jawabin nasa, Dr. Raisi ya jaddada cewa gudanar da sallar jam'i da juma'a na da ayyukan masu tasiri da dama a cikin al'amuran mutum, zamantakewa, tattalin arziki, siyasa da dabi'u, kuma dole Al'umma su kula da ayyukan sallah.


Shugaban ya ce: Kula da yin Sallah da raya Ladubban Sallab mai haske a dukkan matakai na al'ummar musulmi, wata cikakkiyar mafita ce don shawo kan matsalolin da ake fuskantarta Kulawa da gabatar da salloli yana kawar da matsalolin ruhi da jiki da damuwa na zamantakewa da tattalin arziki.


An bude taron Sallolin ne na kasa karo na 29 bayan shafe shekaru 2 ana fama da yaɗuwar cutar Corona a wannan shekara ta kai tsaye da kuma kamar yadda aka saba da saƙon Jagoran juyin juya halin Musulunci.