Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : IQNA
Talata

27 Disamba 2022

20:50:38
1333889

'Yan IMN Sun Halrci Tarukan Bikin Kirsimati Domin Karfafa Zaman Lafiya Tsakanin mabiya Addinai A Najeriya

'Yan kungiyar IMN sun halarci taron bikin kirsimeti a wata majami'a domin taya mabiya addinin kirista murnar zagayowar ranar haihuwar annabi Isa (AS).

Rahotanni daga Najeriya na cewa, 'Yan kungiyar IMN sun halarci taron bikin kirsimeti a wata majami'a domin taya mabiya addinin kirista murnar zagayowar ranar haihuwar annabi Isa (AS).

An dai gudanar ad taron ne a wata majami'a da ke unguwar Samaru Zaria, inda mabiya addinin kirista suka taru domin tunawa da wannan rana, yayin da wasu daga cikin mambobin IMN suka halarci wurin.

Kungiyar IMN dai tana bayyana dalilin halartar wadannan taruka a matsayin daya daga cikin hanyoyi na karfafa zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai.

Wanann dai ba shi ne karon farko da mambobin IMN suke halartar irin wadannan taruka ba, koa  shekarun baya ma sun halarci irin wadannan taruka, lamarin da mabiya addinin kirista suka marhabin da shi.


342/