Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : IQNA
Laraba

21 Disamba 2022

21:25:48
1332827

Minista a Kenya ya kare hijabin da mata musulmi suke sakawa

Aden Duale, ministan tsaron kasar Kenya, ya goyi bayan sanya hijabi da mata musulmi ke yi a kasar, yana mai cewa al'adun musulmi sun nuna cewa matansu su sanya hijabi a bainar jama'a.

Kamfanin dillancin labaran ABNA ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Tuko cewa, Duale wanda ya gabatar da jawabi a masallacin Jamia da ke birnin Nairobi ya ce: sanya hijabi ya dace da al’adar musulmi. A bisa wannan al'ada, dole ne matan musulmi su fito fili da hijabi ko lullubi.

Duale, wanda shi ma musulmi ne, ya ce a wannan taron, wanda aka gudanar a bikin bayar da agaji ga kungiyar agaji ta Red Cross ta Kenya: Eid al-Fitr zai kasance ranar hutu a duk inda gwamnati ta yarda. Gwamnati na mutunta al'adun musulmi. Dole ne mu tabbatar da cewa 'yan matanmu ('yan matan musulmi) sun sanya hijabi.

Yayin da yake jawabi ga masu adawa da hijabi a kasar nan, ya ce: Idan kuna da matsala da hijabi, 'ya'yanmu mata da matanmu suna sanya hijabi. In ba haka ba gara ka bar kasar nan domin su sa hijabi.

A shekarar 2019, batun sanya hijabi ga mata da 'yan mata musulmi ya dauki hankula sosai bayan da makarantar sakandaren Thara mallakar Katolika ta kasar da ke gundumar Murenga ta kori dalibai saboda rufe kawunansu da hijabi. Wannan batu ya haifar da tattaunawa kan 'yancin da mata musulmi ke da shi na sanya hijabi.

Al'ummar Kenya kusan mutane miliyan 55 ne kuma kusan kashi 11% na mutanen kasar musulmi ne.


342/