Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Talata

20 Disamba 2022

11:44:51
1332413

Sojojin Siriya 2 sun jikkata a harin da 'yan sahayoniya suka kai a Damascus

Sojojin Siriya 2 ne suka samu raunuka sakamakon harin da dakarun yahudawan sahyuniya suka kai a wajen birnin Damascus a safiyar yau Talata.

Kamfanin dillancin labaran Ahl al-Bait (AS) ABNA ya nakalto cewa, wasu sojojin kasar Siriya biyu sun jikkata sakamakon harin da aka kai da safiyar yau din nan na gwamnatin sahyoniyawan a wajen birnin Damascus.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na SANA ya bayar da rahoton cewa, rundunar tsaron sararin samaniyar kasar ta yi nasarar dakile makaman roka da gwamnatin sahyoniyawan ta harba a sararin samaniyar birnin Damascus daga wurare daban-daban tare da lalata mafi yawansu.


Wani jami'in sojan Syria ya shaidawa SANA cewa: Da misalin karfe 00:30 agogon kasar a ranar Talata makiya Isra'ila sun yi ruwan bama-bamai a yankunan da ke kusa da birnin Damascus da makamai masu linzami daga arewa maso gabashin tafkin Tiberias, sojojin tsaron sama namu sun kakkabe makamai masu linzami kuma ya lalata wasu daga cikinsu.


Wannan jami’in na Syria ya sanar da cewa, sakamakon wannan harin, an jikkata wasu sojojin kasar Syria guda biyu tare da lalata wasu kayayyaki a yankunan da abin ya shafa.


Kafafen yada labarai sun rawaito cewa rokokin gwamnatin sahyoniyawan sun auka a wasu wurare a kudancin Damascus da kuma kusa da titin filin tashi da saukar jiragen sama na wannan birni.


A cewar jaridar "Yediot Aharonot" na yaren Ibrananci, wannan shi ne hari na hudu da gwamnatin Sahayoniya ta kai a cikin makonni 2 da suka gabata.