Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Asabar

3 Disamba 2022

10:41:02
1328139

Iraq: Bagadaza Na Ci Gaba Da Kokari Kan Sasanta Tsakanin Iran Da Saudiyya

Ya tabbata Iran da Saudiyya na cikin tsarin kokarin Iraki a wannan fanni don gani an sasanta tsakaninsu.

A wata hira da ya yi da shafin yada labarai na Al-Malouma ya bayyana cewa: Tafiyar As Saudany zuwa Tehran ta haifar da wani muhimmin fanni na siyasa da na soji a yanayin da dukkanin kasashen yankin ke bukatar kwanciyar hankali. Matakan da Saudany ya dauka na samun kwanciyar hankali da rage tashin hankali ta hanyar hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa zai hana yankin shiga yaki.

Wannan wakilin na Iraqi ya bayyana cewa, "hadin gwiwa tsakanin Bagadaza da Tehran zai samar da kwanciyar hankali a yankin da kuma tabbatar da tunkarar gwamnatin Iraki ta wannan hanya". Al-Khazraji ya kara da cewa, Saudany ya jaddada daukar manufar nuna tsaka-tsaki ga al'amurran da suka shafi shiyya-shiyya da na kasa da kasa da kuma ci gaba da samun kusanci tsakanin Saudiyya da Iran domin karfafa alaka da rage zaman dar-dar a tsakanin kasashen yankin.