Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Asabar

3 Disamba 2022

10:30:39
1328134

An Kama Wani Malamin Shi'a Na Saudiyya A Madina

Wani mai fafutukar siyasa a kasar Saudiyya ya sanar da kama dan Ayatullah Muhammad al-Omari a Madina.

Kamfanin dillancin labaran Ahlul Bayt As Abna ya nakalto maku cewa, wani dan gwagwarmayar siyasar kasar Saudiyya ya sanar da kame Sheikh Kazem Al-Omari dan Ayatullah Muhammad Al-Omari a birnin Madina.


Dan gwagwarmayar siyasar Saudiyya Ali Hashem ya bayyana cewa jami'an tsaron Saudiyya sun cafke Sheikh Kazem al-Omari yayin da 'ya'yansa biyu ke tsare tun ranar 8 ga watan Afrilun wannan shekara.


Sheikh Al-Omari kuma dan Sheikh Mohammad Al-Omari ne, daya daga cikin fitattun mutane a Madina.


Kasar Saudiyya dai ta tsananta kame-kame da dalilai na siyasa da kuma gurfanar da marubutan siyasa da masu fafutuka a shari’a tare da hukunta su, musamman a yankin Sharkiyeh dake kasar.