Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Talata

25 Oktoba 2022

15:27:49
1317027

An Yanke Hukuncin Kisa Ga Wanda Ya Kai Harin Bam A Kan Hanyar Maziyarta mam Kazem (a.s.)

Wata kotu a Er Bagadaza ta yanke hukuncin kisa kan wanda ya kai harin bam a cikin mota a kan hanyar maziyarta Imam Musa Kazem (a.s.) a yankin Al-Dura.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul Baiyt As - ABNA- habarta cewa, kotun hukunta manyan laifuka ta Al-Karkh da ke birnin Bagadaza ta yanke hukuncin kisa ga wanda ya kai harin bam a cikin mota a kan hanyar Maziyarta Imam Musa Kazem (AS) a yankin garin Al-Dura.


Kamfanin dillancin labaran Irak (Wa,a) ya habarta cewa, bisa nakaltowa daga shafin sadarwa na yanar gizo na hukumar kula da harkokin shari’a ta kasar Iraki cewa, wannan dan ta’addan ya yi yunkurin tayar da wata mota makare da bama-bamai a yankin Al-Dura a daidai lokacin da ake tunawa da shahadar Imam Kazem (AS). wanda wasu ‘yan kasar da suka yi shahada wasu kuma suka jikkata


An zartar da hukuncin ne bisa tanadin sashe na 4 na dokar yaki da ta'addanci a Iraki.