Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : IQNA
Litinin

24 Oktoba 2022

21:02:26
1316904

Mauritania; Nouakchott Babban birnin al'adun Musulunci a 2023

Ministan al'adu na Mauritania ya sanar da fara shirye-shiryen gabatar da Nouakchott a matsayin babban birnin al'adun Musulunci a shekarar 2023.

Kamfanin dillancin labaran ABNA ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Sahra Media cewa, ministan al'adun kasar Mauritaniya Mohamed Oulad Aswaidat ya bayyana cewa: Wannan ma'aikatar ta fara shirye-shirye a aikace domin Nouakchott ta zama hedikwatar al'adun muslunci a shekarar 2023.

Ministan al'adu na kasar Mauritania ya bukaci kasashe mambobin kungiyar ISESCO da su taimaka wajen tsara ayyukan wannan taron.

Da yake jawabi a wajen taron ministocin yada labarai na kungiyar kasashen musulmi da aka gudanar a kasar Turkiyya, ya bayyana cewa, an zabi Nouakchott a matsayin hedkwatar al'adun muslunci a shekarar 2023 bisa kudurin kungiyar raya ilimi da al'adu da kimiyya ta Musulunci ta ISESCO.


342/