Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Alhamis

20 Oktoba 2022

15:46:54
1315560

Ganawar Kwararru Da Manyan Masu Basirar Kimiyyar Iran Da Jagora

Jagora: Shekaru 40 Na Ci Gaban Da Aka Samu Yana Nuna Ingancin Nazarin Juyin Juya Halin Musulunci Ga Duniya

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya kuma jaddada cewa malamanmu ba su bari kasar ta ci gaba da kasancewa cikin bukatuwar turawa ba, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ce: ba tare da wani wuce gona da iri ba, manyan malamanmu na ba da gudummawa ga martabar Iran, kuma a kowane fanni masana kimiyyar mu sun shiga kuma sun mayar da hankali, sun jawo sha'awar al'ummomin kimiyya na duniya, don haka ya kamata wasu ma su yaba, su san girman ku, kuma kuma kusan girman kanku, kuma na yaba da kokarin ku.

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (AS) - ABNA - ya habarta cewa, a safiyar jiya Laraba 19 ga watan Oktoban shekara ta 2022 ne daruruwan matasa masu fada aji da kwararrun masana kimiyya na kasar Iran suka gana da Jagoran juyin juya halin Musulunci.

       


A cikin wannan ganawa, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya kira manyan malamai a matsayin abin da ya haifar da kima da martabar kasar Iran a cikin shekaru arba'in da suka gabata inda ya kara da cewa: Wajibi ne kowa da kowa musamman jami'ai da masu fada a ji a kasar su dauki manyan malamai a matsayin daya daga cikin muhimman kadarorin masu daraja na kasar, tare da kuma tallafa musu tare da karesu, su ma jiga-jigan masanan su yi aiki tukuru tare da mayar da hazakarsu ta daidaiku zuwa ga abunda zai ci gabantar da kasa.Yayin da yake ishara da kyakkyawar makoma a kasar, ya jaddada cewa: A cikin shekaru arba'in da uku da suka gabata, sun yi ta magana (abokan gaba) kan rugujewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran sau da yawa, to amma kwanciyar hankali da ci gaba da yunkurin juyin juya halin Musulunci ya nuna cewa wannan bincike nasu da hasashe ba daidai ba ne kuma ba gaskiya ba ne.


Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana matukar godiya ga Ubangiji da ya sake shirya taron cikin farin ciki da fatan alheri a ko da yaushe tare da masu fada a ji bayan an samu saukin matsalar corona inda ya ce: batutuwan da manya suka gabatar suna da kyau kwarai da gaske kuma shawarwarin sun kasance daidai kuma galibi masu amfani ne. kuma ya nuna akwai matsaloli da yawa a cikinsu amma matsalolin gudanarwa ne wanda ya kasance akwai mafita tattare da su.


Ya umurci ministocin da suka halarci taron da su mika kundin da aka bayar tare da bibiyar shawarwarin da masu fada aji a majalisar ministocin suka bayar, ya kuma kara da cewa: Mu yi aiki tukuru wajen kula da wannan kudiri mai muhimmanci da kuma kara yawan tasu ta hanyar daukar manyan mutane a matsayin wata babbar arzikin kasa.


Ayatullah Khamenei ya dauki manyan malamai da jami'a a matsayin muhimman ginshikan ci gaban kasar sannan ya kara da cewa: duk yadda jami'a ta kasance a rufe da kuma rugujewar ayyukan ilimi da rashin cikawa to hakan zai zamo dama ce ga makiya, shi ya sa to sun yi kokari ba jiya da yau ba a lokuta daban-daban don hana gudanuwar jami'o'in.


Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya kuma bayyana jami'ar a matsayin daya daga cikin manya-manyan abubuwan da ke kawo cikas ga mamayar girman kai ya kuma kara da cewa: ma'abota karfi na duniya suna amfani da makamai da yaudara har ma da kimiyya wajen mamaye wasu da kuma mayar da al'ummomi baya, don haka duk jami'ar da ta daga darajarta na kimiyyar kasar a zahiri ta zamo cikas ga mamayar makiya.


Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya kira hazaka ta dabi'a da wadatar hankali da himma da kokari da tsayin daka da kuma shiriya da nasara na Ubangiji a matsayin manyan abubuwan da ke tabbatar da mayar da mutum mai hankali zuwa ga wani fitaccen mutum, fitaccen mutum kuma zababben mutum sannan ya kara da cewa: Tabbas samar da sahihin asali shi ne muhimmin al'amari don samun sakamako ga wajen kaiwa ga wannan yanayin.


Jagora ya kira kafa fagen ilmantarwa tare da nasarar juyin juya halin Musulunci a matsayin tabbataccen lamari da babu kokwanto a cikinsa, sannan ya kara da cewa: Bayan nasarar juyin juya halin Musulunci, tare da ci gaban jami'o'i a dukkan sassan kasar, an samu karuwar dalibai masu ban mamaki da kuma ban malami da Farfesoshi da samar da cibiyoyi masu yawa na bincike da cibiyoyin nazari an samar da filin ci gaban ilimi da sanin makamar aiki, sannan kuma manufar Jamhuriyar Musulunci ta fadada jami'a da inganta ilimin kimiyya ya samu nasara bisa falalar Allah Ta'ala.


Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya kuma jaddada cewa malamanmu ba su bari kasar ta ci gaba da kasancewa cikin bukatuwar turawa ba, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ce: ba tare da wata mubalaga ba, manyan malamanmu na ba da gudummawa ga martabar Iran, kuma a kowane fanni masana kimiyyar mu sun shiga kuma sun mayar da hankali, sun jawo sha'awar al'ummomin kimiyya na duniya, don haka ya kamata wasu ma su yaba su san girmanku, su san ku, kuma kusan girman kanku, kuma na yaba tare da girmamaku da ayyukanku.


A yayin da yake bayyana wasu daga cikin karramawar fitattun mutane da masana kimiyya na kasar, ya ambaci bincike da nasarorin da Cibiyar Bincike ta Royan ta samu a fannonin da suka hada da kwayar halitta mai rai (Stsel cells) da cloning na dabbobi masu rai, ci gaban kimiyyar halittu, harba tauraron dan adam zuwa sararin samaniya, nasarorin da aka samu a sararin samaniya. Masana'antar nukiliya, samar da hadaddun rigakafi daga cikinsu, ya yi nuni da rigakafin Corona da ci gaba mai ban sha'awa a masana'antar roka da jirage masu saukar ungulu.


Ayatullah Khamenei ya nanata cewa mutane masu hankali da suka yi amfani da basira da iliminsu wajen kera makaman nukiliya, makamai masu guba, ko kayan aikin leken asiri, ba su ne fitattun mutane ba, ya kara da cewa: Manyan mutane su ne hazikan mutune masu kwazo da suka ci gajiyar shiriyar Ubangiji.


Daga nan sai ya tabo batun “fatan da ake da shi daga manyan mutane” inda ya ce: akwai fata da ake da shi daga zababbun mutane wanda shine ya mayar da karfinsa na kashin kansa zuwa matsayin na kasa da kuma yin amfani da karfinsa wajen magance matsalolin kasar.


Jagoran juyin juya halin Musulunci ya koka kan wasu zababbun mutane da suke girma a kasar Iran amma suna fitar da amfanin wannan ci gaban zuwa ga kasashen waje, wani lokacin kuma suna ba wa makiya kokarinsu, sannan ya kara da cewa: Kamata ya yi su kasance su zauna tare da al'ummarsu. Tabbas babu laifi su yi hijira ya yi karatu a manyan jami'o'i, amma bayan ya kammala karatunsa sai ya koma kasar ya yi amfani da iwarsa kwarewarsa wajen ci gaban kasa.


Ayatullah Khamenei ya jaddada cewa: Wajibi ne zababbun mutane su warware wannan lamari a a kashin kansu da kuma gaban Ubangiji.


Sannan, Wani abin da ake fata daga zababbaun mutane a matsayin su shine “kada suyi sakaci da shiga gafala” sannan ya ce: Kada manyan malamai su yi sakaci da iya karfinsu don kada kokarinsu da motsinsu su tsaya, kuma kada su zama ‘yan kame-kame na nishadi masu cutarwa.


Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya dauki rashin yin watsi da irin wannan gagarumin aiki na kasar a matsayin wani abin da ake bukata na zabbbaun mutane sannan kuma ya kara da cewa: Abin bakin cikin shi ne mafi yawan zababbun mutanen ba su da masaniya game da irin girman irin karfin da kasar ke da shi, kuma daya daga cikin muhimman ayyuka Mataimakin ilimi na shugaban kasa shi ne ya sanar da zababbu matasa masu kokari da iya aiki da manyan ayyuka da aka gabatar.


Ayatullah Khamenei ya yi ishara da cewa: Har ma wasu mutane suna musunta irin gagarumin karfin da kasar ke da shi, suna ma neman a tattara karfin da ake da shi kamar masana'antar nukiliya, suna masu karyar cewa duniya a yau ta kau da kai daga masana'antar makamashi da makamashin nukiliya.


Ya jaddada cewa: Idan ba a lokacin da muka fara aikin nukiliya mun farashi alokacin ba, to da yakamata mu shiga wannan batu bayan shekaru 10, kuma mu kai ga cimma matsaya bayan shekaru 30.


Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi la'akari da cewa rashin gafala ga makiya a matsayin daya daga cikin hatsarin da ke fuskantar masu kokari zababbun wannan Al'umma yana mai cewa: Bisa ingantattun bayanai, jami'an leken asiri suna masu kokarin yaudarar da farautar manyan masu ilimi ko kuma wargaza tunanin kwakwalensu suna masu fakewa da cibiyoyin ilimi don yaudara da jawo hankalin masu Ilimi ko kuma lalata Hankalinsu, suna bin abin cikin nutsuwa da hankali don su ci gaba da shirinsu.


*Ya* ci gaba da yin tsokaci kan abin da ake sa ran daga cibiyoyin da ke da alhakin kula da zababbu: A dunkule, babban abin da ake bukata daga cibiyoyi shi ne tallafawa zababbun cikin hikima da hankali tare da la’akari da bangarori daban-daban.


Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ci gaba da cewa: Daya daga cikin abin da za a ba da goyon baya shi ne yadda manyan da suka yi karatu a ciki ko kuma suka zo daga ketare, za su iya samun aikin yi a nan gwargwadon iliminsu, da kuma yiwuwar gudanar da bincike da sadarwa tare da cibiyoyin kimiyyar duniya, kuma wannan bai da wani karfi sosai.


Haka nan kuma yayin da yake ishara da sake hijira na wasu fitattun mutane da suka dawo daga ketare, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya yi jawabi ga jami'an inda ya ce: Kada mu bari manyan malamai su karaya daga jami'a da ci gaba da gudanar da ayyukansu a cikin kasar saboda wasu jifa da jifa da ba su dace ba, kuma duk abunda muka kashe a wannan fanni, ba dawainiya ce mai wahala ba, illa zuba jari.


Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya jaddada wajabcin yin kwaskwarima ga ma'aunin tantance furofesoshi da zababbun masana inda ya ce: A yanzu ma'aunin tantance malamai da manyan malamai shi ne adadin makaloli, yayin da warware matsaloli ya kamata a yi la'akari da shi a matsayin ma'aunin kyautatawa.


A bangare na karshe na jawabin nasa, Ayatullah Khamenei ya yi tsokaci kan wani lamari na asasi dangane da daidaitattun lamurra, da gyara mahangar hangen nesa da motsawa a kan haka.


Haka nan kuma yayin da yake ishara da farfagandar da Turawan Yamma suka ci gaba da yi tun daga farkon nasarar juyin juya halin Musulunci har zuwa yau na cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana kara tabarbarewa, sai ya ce: Sun sanya iyakar lokaci kan wannan da'awar, kuma a duk lokacin da suka ce nan da wata guda ko nan da shekara guda ko kuma nan da wasu shekaru biyar, aikin jamhuriyar Musulunci zai kare ya cika, kuma harma wasu mutane suka yada wadannan da'awar a cikin gida saboda sakaci ko qeta tare da yadata.


Haka nan kuma yayin da yake ishara da kanun labaran da wata jarida ta wallafa a lokacin rayuwar Imam da ke cewa "tsari yana rugujewa" da kuma amsa mai ban mamaki da Imam ya bayar na cewa "kai kanka ne kake rugujewa alhali tsarin yana nan tsaye kyam" ya kara da cewa: Bayan rasuwarsa a shekara ta 1369 wasu mutane daga cikin su wadanda kuma akwai wasu barata kuma gogaggun mutane, sun ce a cikin sanarwar cewa "tsarin yana tsaye kyam".


Ayatullah Khamenei ya jaddada cewa: Ba mu yi kasa a gwiwa ba, mun tsaya, kuma in Allah Ya yarda za mu ci gaba da tsayin daka.


Yayin da yake ishara da samuwar tsare-tsare na nazari guda biyu a cikin wannan fage, ya ce: akwai tsarin nazari da ya yi imanin cewa aiki da Gwagwarmaya a gaban ka'idoji na duniya da kuma karfin da suke taso daga wadannan ka'idoji, kamar Amurka, ba shi da wani amfani kuma yana haifar da halaka, wadannan mutane masu suna yiwa waɗanda da suke da wani nazarin ta fuskacin duniya, suna da ra'ayin ruɗi na gaskiya da duniya.


Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ce: To amma masu nazari na biyu kuma na hakika ya ginu ne a kan cewa yana ganin jigo na hakika, ba wai kawai ingantattun hujjoji ba, har ma da munanan hujjoji, kuma akan haka yake gudanar.


Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: Ba mu taba yin inkarin raunata ba, kuma a kan haka mun yi ishara da fiye da komai a tarukan watan Ramadan na jami'an gwamnatin kasar da kuma a ganawar sirri, kuma mun sha bayyana cewa muna baya.


Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ci gaba da cewa: To amma abin mamaki shi ne cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta ci gaba da tafiyar da ayyukanta cikin sauri da ta fara tun daga karshen ayarin kuma a yau ta isa gaban ayarin.


Da yake ishara da irin gagarumin ci gaban da kasar nan ta samu a fannin ilimi da gudanarwa daban-daban, ya ce: Akwai raunin da wasu jami'ai da gwamnatoci suka yi, amma gaba daya yunkuri na neman ci gaba ne.


Ayatullah Khamenei ya yi ishara da cewa: Ku duba a ina Jamhuriyar Musulunci ta kasance shekaru 40 da suka gabata ko kuma shekaru 20 da suka gabata da kuma inda take a yau, da wannan kwatancen za ku iya fahimtar wane bincike ya tabbata, shin nazartar turawan yamma ne ko kuma nazarin juyin juya halin Musulunci?


Ya dauki matasa da zababbun Malamai a matsayin daya daga cikin manya-manyan alamomin yunkuri mai karfi da ci gaba na juyin juya halin Musulunci ya kuma kara da cewa: Bayan shekaru gomomi 4 na juyin juya halin Musulunci duk da yawan gaba da farfaganda maras kyau, amma hakan bai hana samuwar manyan gwanaye wadanda suke da yawa da yin imani da wannan tafarki kuma suna aiki da gaske kuma kokarinsu shine mafi kyawun dalili na daidaiton nazarin juyin juya halin ga duniya da kuma ingantacciyar hanyar ci gaba.


A farkon wannan ganawa dai wasu manyan Zababbun Masana matasa 7 ne suka bayyana ra'ayoyinsu da da suka hada da maza da mata:


- Amir Muhammadzadeh Lajordi - dalibin gaba da digiri a fannin software a jami'ar Sharif


- Hamidah Majed - zababben daya daga cikin Shahid Ahmadi Roshan National Elite Foundation kuma mai fafutuka a fannin hakar ma'adinai.


- Jawad Shams al-Dini - matsayi na 65 a jarrabawar shiga jami'a a fannin likitanci kuma memba a kungiyar National Elite Foundation.


- Muhammad Temanai- PhD a fannin Injiniya sufuri, Jami'ar Tarbiat Mudares


- Zahra Ehtsham - wacce Shahid Ahmadi Roshan project ya zaba kuma daliba mai hazaka.


- Sayyed Muhammad Naweed Qureshi - Ph.D. a Injiniya Aerospace, Jami'ar Tehran


- Wahid Zarghami - PhD a cikin Nanotechnology, Jami'ar Fasaha ta Sharif


Sun bayyana wadannan nazarori kamar haka:


- Bukatar ci gaba a cikin abubuwan more rayuwa na hako ma'adinai da amfani da su tare da sa hannu na kamfanoni masu zaman kansu tare da mutunta matsalolin muhalli.


- Rage harajin shigo da kayayyaki na manyan injuna da masana'antun ke buƙata waɗanda ba su da abin da ake samarwa a cikin gida


- Bukatar inganta daidaito na ilimi da kuma kafa tsare-tsare na musamman don tallafawa ilimi a yankunan da ba su da shi.


- Sukar karuwar kwatsam a cikin karbar ɗaliban likitanci ba tare da shirya abubuwan da suka dace ba.


- Ba da shawarar samar da dabarun zirga-zirgar ababen hawa don kammala ayyukan sufuri da kuma mayar da Iran cibiyar sufurin yankin.


- Bukatar samar da alaka tsakanin batun bunkasa ilimi a manyan makarantu da magance matsalolin kasar.


- Wajabcin samun canji a cikin shirye-shiryen sararin samaniya, musamman tallafin kuɗi akan sikelin ƙasa da ƙarfafa abokan hulɗa na duniya.


- Wajabcin samar da manufofi kan ci gaban kamfanoni masu dogaro da kai a sassan da ke da bukatu da kasuwa da samar da sha'awa ga jarin jama'a masu riba.


A cikin wannan ganawar mukaddashin shugaban kasa a fannin kimiyya da fasaha, Dakta Dehghani Firouzabadi, ya dauki harkar kimiyya a kasar a matsayin wani sakamako na samar da lamurra da kuma gagarumin kokarin jagoran juyin juya halin Musulunci a shekarun da suka gabata. Ya kuma yi ishara da bukatar ci gaban masana'antu masu dogaro da kai, domin karfafa tafarkin ya ce: Farfado da masana'antu na ilimi bisa ka'idar yawaita kirkira, hadin gwiwa da hanyoyin sadarwa na ilimi, tallafawa wajen samar da fasahohin cikin gida. sannan hana shigo da kaya daga waje na cikin ajandar gwamnati.