Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Alhamis

20 Oktoba 2022

09:19:42
1315525

Ministan Harkokin Wajen Saudiyya: Ba Ma Tsoma Baki A Harkokin Cikin Gidan Iran

Dangane da tashe-tashen hankulan da suka barke a Iran a baya-bayan nan, Ministan Harkokin Wajen Saudiyya ya jaddada cewa, manufar Riyadh ba ta tsoma baki cikin harkokin cikin gidan wasu kasashe ba ne.

Kamfanin dillancin labaran Ahlul Bayt As ABNA ya habarta cewa, ministan harkokin wajen kasar Saudiyya Faisal Bin Farhan, a wata tattaunawa da ya yi da tashar talabijin ta Al-Arabiya, yayin da yake amsa tambaya kan tashe-tashen hankula da abubuwan da suka faru a Iran a baya-bayan nan, ya ce: Tsayayyen manufofinmu shine rashin tsoma baki cikin harkokin cikin gidan wasu kasashe, kuma Riyadh ba ta Nufin bayyanar da raayinta Dangane da hakan"Ministan harkokin wajen Saudiyya ya ce: Muna fatan alheri ga Iran da al'ummarta.


Yayin da yake ishara da shawarwarin Tehran da Riyaad ya ce: An gudanar da shawarwari guda biyar a tsakanin kasashen biyu, kuma bangarorin na yin nazari tare da tantance wadannan tattaunawa ta yadda za a iya gudanar da zagaye na gaba Kuma Riyadh da gaske take game da buɗe batun tattaunawar.