Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : IQNA
Talata

18 Oktoba 2022

20:27:03
1315105

Fushin Isra'ila kan matsayin Australia akan Kudus

Gwamnatin Australia ta ki amincewa da Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila; Wani mataki da ya harzuka Isra'ila.

A rahoton da jaridar Middle east ta bayar, ministar harkokin wajen Australiya Penny Wong, inda ta yi nuni da cewa ofishin jakadancin kasarta zai ci gaba da zama a birnin Tel Aviv, ta sanar da cewa, Quds wani muhimmin batu ne da ya zama wajibi a tantance shi a tsarin shawarwari tsakanin bangarorin Palasdinu da Isra'ila.

Ta kuma jaddada cewa, kasarta za ta ci gaba da yin aiki tukuru wajen ganin an kafa kasashe biyu.

Bayan wannan mataki, Isra'ila ta gayyaci jakadan Australia a yankunan da ta mamaye.

Firaministan Isra'ila Yair Lapid ya mayar da martani kan wannan mataki na Australia ya kuma ce, bayan wannan mataki na Ostireliya, mutum na iya fatan cewa gwamnatin Australia za ta yi taka tsan-tsan a wasu batutuwa.

Ya kara da cewa: Kudus (Quds) ita ce tabbatacciyar hedkwatar Isra'ila kuma babu wani abu da zai iya canza wannan lamari.


342/