Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : IQNA
Alhamis

13 Oktoba 2022

21:17:52
1313499

Lamarin Falastinu ya saka Isra’ila a cikin firgici

Kungiyar Hizbullah ta Lebanon ta ce ba za ta amince da duk wata yarjejeniya ta kan iyakokin ruwa tsakanin Lebanon da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ba har sai an sanya hannu a kai a hukumance.

Kalaman na babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyed Hassan Nasrallah na zuwa ne a daidai lokacin da rahotanni ke cewa Lebanon da Isra'ila sun amince da daftarin yarjejeniyar.

Sakatare-Janar na kungiyar Hizbullah Sayyed Hassan Nasrallah ya bayyana a daren jiya Talata cewa, sa'o'in da ake jira suna da uhimmanci, a matsayinmu na al'ummar kasar Labanon, muna jiran a bayyana amincewa da yarjejeniyar ne a hukumance daga bangaren shugaban kasar Lebanon, a lokacin ne za mu amince da ita.

Ya ce "za mu ci gaba da yin taka-tsan-tsan" har sai an kammala yarjejeniyar, yana mai cewa ya kamata yarjejeniyar da ta dace da bukatun gwamnatin Lebanon.

Nasrallah ya ce: "Abin da ke da muhimmanci ga bangaren ‘yan gwagwarmaya shi ne al'ummar Lebanon su sami damar hako mai da iskar gas daga filayen kasar."

Har ila yau, a ranar Talata, wani babban dan majalisar Hizbullah ya ce, tsayin dakan da Lebanon ta yi kan wannan batu, ya tilasta wa Isra’ila ja da baya, ala tilas kuma ta amince da sharuddan Lebanon a hukumance.

Dangane da batun Falastinu kuwa, Sayyid Nasrullah ya bayyana cewa, abin da yake faruwa a halin yanzu a yankunan yammacin gabar kogin Jordan ya tabbatarwa Isra’ila da cewa ba za ta iya murkushe gwagwarmayar al’ummar falastinu ba, duk kuwa da irin cikakken goyon bayan da take samu kan hakian daga manyan kasashen turawa.


342/