Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ABNA24
Laraba

12 Oktoba 2022

20:30:59
1313136

Nawab: Aiki Da Koyarwar Addini Yana Haifar Da Hadin Kai

Wakilin Waliyul Faqih a fagen aikin Hajji da Ziyara ya bayyana cewa: A cikin koyarwar kyawawan halaye mun shaida wannan lamari cewa soyayya tana da matsayi mai fadi da girma a Musulunci, haka nan kuma Manzon Allah (SAW) ya kasance gwanin soyayya ga kowa da kowa na mutane don haka addinin Musulunci addinin soyayya ne, kuma addini shi ne kawar da dalilan sabani.

  Kamfanin dillancin labarai na Ahlul Bayt (A.S) - ABNA - ya kawo maku rahoton cewa: Hujjatul-Islam Wal-Muslimeen, Seyyed Abdul Fattah Nawab, wakilin Wilayatul Fakihp a fannin aikin hajji da Ziyara, a webinar na shida na Taron hadin kan kasa karo na talatin da shida, yayin da ake girmama makon hadin kai da maulidin Manzon Allah (SAW) da Imam Jafar Sadik (A.S), ya bayyana cewa: A hakikanin gaskiya Allah mai girma ya sanya addinin Musulunci ya zama addinin hadin kai da daidaito zamowa abu guda, kuma dukkan koyarwar addini, ko koyarwar kyawawan halaye, fikihu da hukunce-hukunce, sakamakonsa ne kuma sun samo asali ne daga wadannan ayyuka.

Ya kara da cewa: A cikin koyarwar kyawawan halaye, mun shaida lamarin cewa soyayya tana da matsayi mai fadi da girma a Musulunci, haka nan kuma masoyin Musulunci (SAW) ya kasance mai soyayya ga dukkan mutane, don haka Musulunci shi ne addinin soyayya da kaunar juna, addinin kawar da duk wani dalilai na sabani.

Hujjatul-Islam Nawwab Islam ya ci gaba da cewa: Karya, zage-zage, kage duk wadannan hanyoyi ne na rarrabuwar kawuna da samun sabani kuma sun kasance haramun ne a addini, a daya bangaren kuma, gaskiya, tawali'u da soyayya, dalilai ne na samar da soyyaya kuma suna bangare na koyarwar addini.Saboda haka, muna ganin cewa mas'aloli na kyawawan halaye suna da haɗin kai da kansu kuma suna haifar da haɗin kai.

Wakilin Waliyul Faqeh addini a fagen aikin Hajji da Ziyara ya bayyana cewa: Dangane da fikihu da mas’alolin addini, muna ganin cewa babban matsayin sallah shi ne yin salla tare, wani lokacin kuma musulmi suna yin salla a masallacin Annabi (SAW), masallacin Harami. ko kuma wasu gurare.kuma muna ganin dukkan addinai suna yin sallar jam'i a lokaci guda da wuri guda a wata hanya ta musamman, don haka dukkan wadannan abubuwa suna hadewa da juna ne.

Ya bayyana cewa a lokacin aikin Hajji musulmi duk suna kusa da juna tun daga farko idan sun shiga miqat ba a raba su kuma a wani lokaci sai su zama suna cikin ihrami, ya ce: Duk musulmin da suke aikin Hajji suna sa tufafi iri daya ne kuma kala iri daya. suna nan kusa da juna, zikirin da suke cewa kowa daya ne, hatta alkiblar dawafin Ka'aba daga bangare guda yake, don haka halayya da shari'a suna da dalilan samar da hadin kai a duniyar Musulunci.

Hujjatul-Islam Nawwab ya ci gaba da cewa: A daya bangaren kuma, duk munanan dabi'u an yi watsi da su, kuma Musulunci bai yarda da su ba saboda wadannan dabi'un da ke haifar da sabani ko dai daga ran mutum ne ko kuma daga Shaidan. Idan sanadin Sabani Ya samo asali ne daga ruhin mutum ne, to hakan zai haifar da rikici da rashin jituwa.

Wakilin waliyul fikih a fagen aikin Hajji da Ziyara ya yi nuni da cewa: Manzon Allah (SAW) dangane da Jadaal da Mara’a yana cewa: ku bar yin Jayayya domin shi mumini baya jayayya”.

Ya ci gaba da cewa: Sayyidina Ali (a.s) yana cewa: Sakamakon husuma da jayya shi ne yana haifar da rarrabuwa, kuma rashin hadin kai ya sabawa hadin kai da ‘yan’uwantaka. A gaskiya ma jayayya mummunan cuta ne, kuma ga mutane, babu wani hali mafi muni fiye da wannan.

Hujjatul-Islam Nawwab Islam ya ce: Jayayya tana daga cikin abubuwan da ya kamata a nisantar da ita a aikin Hajji, a aikin Hajji mu maida hankalimnu wajen bauta wa Allah abin bauta.

Yayin da yake bayyana cewa muna da sabani iri biyu ne, daya jayayyar mai kyau da kuma jayayya abin zargi, wakilin Waliyul fikih a fannin aikin Hajji da ziyara ya kara da cewa: jayayya abin zargi it ce wanda jayayyar ta yi daidai da maslahar kashin kai, kuma Allah madaukaki yana cewa: Ka yi kira zuwa ga tafarkin ubangijika cikin hikima da wa'azantarwa mai kyau.

A karshe ya ce: Nasarar koyarwar halayya da fikihu ta addini ita ce samar da hadin kai da jituwa a tsakanin musulmin dukkanin mazhabobi, kuma abin da ke haifar da munafunci da kiyayya shine nisantar juna, kuma abune ne mara kyau kuma abin ki a ilimi da koyarwar addini.  


342/