Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : iqna
Litinin

3 Oktoba 2022

21:34:27
1310343

Fitar da wakilan Iran zuwa wasan karshe na gasar kur'ani ta Turkiyya

Wakilan kasar Iran sun samu nasarar halartar bangaren karshe na gasar kur'ani ta kasa da kasa karo na 8 da aka gudanar a kasar Turkiyya inda suka tsallake matakin share fage.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, a daren jiya 10 ga watan Oktoba ne masu gudanar da gasar suka fitar da sunayen wadanda suka kammala gasar kur’ani ta kasa da kasa karo na 8 a kasar Turkiyya.

A bisa haka Vahid Khazaei da Hossein Khani, wakilan kasar Iran a gasar kur'ani ta kasa da kasa karo na 8 na Turkiyya a fagen bincike da haddar kur'ani baki daya, sun tsallake matakin share fage tare da samun nasarar halartar bangaren karshe na wannan gasar.

Mahalarta takwas daga kasashen Aljeriya, Morocco, Guinea, Iran, Libya, Syria, Turkey da Yemen, sun halarci matakin karshe a fannin karatun bincike.

Har ila yau, wakilai daga kasashen Aljeriya, Gambia, Iran, Libya, Somalia, Syria, Tajikistan da kuma Yemen suna halartar fagen haddar kur'ani baki daya.

A daren ranar Litinin ne aka gudanar da matakin karshe na wannan gasa kuma ana sa ran za a bayyana sakamakon gasar a cikin kwanaki masu zuwa.

Wakilan kasar Iran za su shigo kasar a farkon mako mai zuwa.


342/