Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

20 Satumba 2022

17:20:14
1306764

​Putin: Kasashen Turai Suna Ji A Jikinsu Sakamakon Takunkuman Da Suka Saka Wa Rasha

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya ce kasashen yammacin duniya da suka kakaba wa Rasha takunkumi suna matukar jin jiki sakamakon tasirin hakan.

Shugaban na kasar Rasha ya bayyana hakan ne a yau a lokacin karbar takardun shaidar kama aiki na sabbin jakadun kasashe 24 a Moscow.

Ya ce kasashen da suke da matukar bukatuwa saboda talauci suna cutuwa sakamakon takunkuman da kasashen turai suka kakaba ma Raha, domin kuwa ba za su iya samun abincin da suke bukata daga Rasha ba, amma kuma a lokaci guda kuma su kansu kasashen turan suna jin jiki, domin kuwa sun haramta wa kansu abubuwa da dama da suke samu daga Rasha.

Ya kara da cewa "tsarin duniya yana canzawa, kuma duniya tana rikidewa zuwa tsari mai dunkulewa, wanda zai zama babbar hanyar ci gaba", ya kuma bayyana cewa, kasashen da ke adawa da wannan sauyi su ne wadanda suke son ci gaba da mulkin duniya da sarrafa tattalin arzikin kasashe da kuma danne al’ummominsu.

Putin ya ce, tun kafin wannan lokacin mun gargadi kasashen turai da cewa, su rika sara suna dubar bakin gatari, domin kuwa duk wani yunkuri na cutar da Rasha, to su ne za su fara cutuwa, kuma hakan zai yi mummunan tasiri ga zamantakewar al’ummominsu, wanda tabbas zai haifar ma ‘yan siyasa masu manyan matsaloli.

342/