Ali Bagheri Kani ya bayyana cewa, akwai batutuwa da suke bukatar yin dubi a kansu dangane da rahoton hukumar kula da makamshin nukiliya na baya-bayan nan akan shirin Iran, wanda har kullum a cewarsa Iran tana yin kira ga hukumar da kuma shugabanta da su guji saka manufofin siyasar wasu kasashe a cikin aikinsu, domin yin hakan zai zubar da mutuncin hukumar.
Tun a jiya ne dai shugaban kasar Iran ya bar birnin Tehran zuwa birnin New York na kasar Amurka domin halartar babban taron na Majalisar dinkin duniya, inda zai gabatar da jawabi a gaban babban zauren majalisar, da kuma ganawa da wasu daga cikin shugabannin kasashe da na gwamnatoci a gefen taron.
342/