Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

20 Satumba 2022

17:18:33
1306760

Ra'isi: Mulkin Mallakar Kasashen Turai Ne Ke Cutar Da Ci Gaban Kasashen Duniya

Ibrahim Rai’si shugaban kasar iran ya fadi cewa kasashen turai masu karfin dafa aji suna hana ci gaba da bunkasar kasahen duniya sakamakon Aladar mamaya da baba kere da suke aiwatar ta hanyar yin amfani da hukumomin na kasa da kasa domin amfanin kansu.

Ra’isa ya yi wadannan kalaman ne a lokacin rufe taron kwanaki 3 kan yada ilimi a gefen taron babban zauren majalisar dinkin dunina a birnin Newyork,

Yace abin takaici Aladar mamaya da kasashen turai ke aiwatarwa yana jawo koma baya ga kasashen duniya daban-daban, suna hana kasashe ci gaba ta hanyar kirkiro wasu dokokin kasa da kasa na rashin adalci , da yin amfani da kungiyoyin kasa da kasa don kare manufofinsu, da bullo da wasu tsare-tsare don tilasta yin amfani da ala’adu da ra’ayoyinsu na son zuciya.

Daga karshe Ra’isi ya yayi kira ga hukumomin kasa da kasa da su girmama ala’adu da hakkin ilimi na kasashen duniya, yace ba zai yi wu A Canza tsarin ilimi ba tare da la’akari da abubuwan masu muhimmacin ba kamar iyalai da daidaito . da kuma hare hakkokinsu daga mulkin mallakar kasashen yamma na Ala’adun

342/