Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

20 Satumba 2022

17:17:41
1306758

Ministocin Harkokin Wajen Iran Da Qatar Sun Jaddada Muhimmancin Fadada Dangantakar Tsakaninsu

Rahotanni sun bayyana cewa ministan harkokin wajen kasar Iran Amir Abdallahiyan da takwaransa na kasar Qatar Mohammad bin Abdulrahman Al-thani sun tattaunawa game da ci gaban da aka samu a tattaunawar da ake yin a farfado da yarjejeniyar nukiliya kasar iran da aka cimma a shekara ta 2015, da kuma hanyoyin da zasu bi wajen kara karfafa dankon zumuncin dake tsakaninsu

A bayan bayan nan kakakin ma’aikatar harkokin wajen iran ya bayyana cewa kwararru daga Tehran da sauran wakilan bangaren tattaunawar ta JCPOA wato Rasha, China, Fransa , Ingila da kuma kasar Jamus mai yi yua su gana agefen taron babban zauren majalisar dinkin duniya karo na 77 domin tattaunawa kan yadda za’a cirewa Iran takunkumin da Amurka ta kakaba mata.

Naseer Kan’ani ya fadi hakan ne lokacin da yake bayani game da halartar taron babban zauren majalisar dinkin duniya da shugaban Iran Ibrahim Raisi zai yi a birnin Newyork tare da babban mai shiga tsakani na kasar Iran Ali Bagheri kani.

Daga karshe ya nuna cewa iran tana amfani da duk wata dama da aka samu wajen bayyana ra’ayoyinta masu muhimmanci , taron babbban zauren majalisar dinkin duniya wuri ne da ya dace da irin wannan damar.

342/