Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

20 Satumba 2022

17:17:14
1306757

Uganda: Majalisa Na Nazarin Kudurin Doka Da Za ta Bada Damar Dashen Sassan Jiki A Kasar

Rahotanni da suka fito daga birnin Kampala na kasar Uganda ya nuna cewa majalisar dokokin kasar Na nazarin wani kudurin doka za ta bayar da damar yin dashen sassan jiki a karon farko a kasar ta gabashin Afrika, wani karamin juya hali ne da zai canza rayuwar dubban mutane dake jiran ayi musu tiyata.

Idan majalisa ta Amince kasar Uganda zata bi sahun sauran kasashen Afrika kamar Afrika ta kudu , Tunusia, da kuma kasar Kenya. Wadanda tuni suke da tsare-tsare da kayan aiki na lafiya da suke bada damar yin dashen sassan jiki a kasashensu.

Kasashen indiya da turkiya ne kasashen da mutanen kasar Uganda suka fi zuwa domin yi musu dashen koda, sai dai yan uwa na kusa kawai ake bari su bada kyauta ku su yi tafiya tare da amincewar cibiyar lafiya ta kasar domin kaucewa fataucin sassan jikin mutane ko kuma tilastawa mutane su bada sassan jikinsu.

Idan dai aka amince da sabon kudurin a majalisar dokokin kasar mataken zai fi zama mai sauki kuma zai rage farashin yin tiyata zuwa dala 800 mai makon dala 30,000 dake kashewa wajen yin dashen gabbai a kasashen waje, kuma za’a kafa bankin adana sassan jiki ga wadanda ke sha’awar bada sauran sassan jiki ba sai koda ba kawai.

342/