Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

20 Satumba 2022

17:16:23
1306754

Najeriya: Kungiyar Daliban Jami’o’i Sun Toshe Hanyar Shiga Tashar Jiragen Sama Ta Lagos

Kungiyar daliban jami’o’ii ta Najeriya ta toshe manya-manyan tituna wadanda suka je tashar jiragen saman ta Murtala Muhammad da ke brnin Lagos a jiya da safe wanda ya jawo jinkirin tashin jiragen sama zuwa wasu garuruwa a cikin gida da kuma kasashen waje.

Jaridar Leadership ta Najeriya ta bayyana cewa abin ya kai ga wasu ma’aikata sun taka da kafa sosai kafin su isa wuraren ayyukansu a tashar jiragen saman. Sai dai hukumomi a tashar sun bayyana cewa babu wani jirgin da ya fasa tashi saboda hakan.

Kamfanin jiragen sama mai zaman kansa na Arik Air ya ce ya jirgkita tashinsa na cikin gida na wani lokaci saboda rashin isar fasinjoji a cikin lokaci saboda toshe titunan.

Kungiyar malaman jami’o’ii ta ASSU dai tana yajin aiki tun kimani watanni 7 da suka gabata, saboda gwamnatin tarayyar ta kasa aikwatar da alkawulan da ta cimma da ASSU.

342/