Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

20 Satumba 2022

17:16:00
1306753

​Ra’isi: Ci Gaban Ilmi A Duniya Ba Zai Yu Ba Sai An Kula Da Iyalai Tun Farko

Shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi, ya bayyana cewa tarbiya da ilmi ba zai samu ba sai tare da kula da iyalai tun farko.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka a jiya Litinin, a cikin jawabinda da ya gabatar a wani taron dangane da bukasa ilmi a duniya wanda hukumar raya al-adu da ilmi da MDD wato UNESCO ta shirya a birnin NewYork na kasar Amurka.

Ra’isi ya kara da cewa a jumhuriyar musulunci ta Iran an gina tsarin ilmi da tarbiya ne tare da lura da al-adu da addinin mutanen kasar Iran, adalci da kuma halaye masu kyau.

Shugaba ya ce wani kokari na wayar da kan mutane ko tarbiya ga wata al-umma ba tare da tabbatar da adalci da kuma kula da addinin da al-adun mutanen kasar ba, wanna zai hana ci gaban ilmi, kamar yadda muke gani a wasu kasashe wadanda aka haramta masu ci gaban ilmi saboda wadanda matsaloli da na ambata.

342/