Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

20 Satumba 2022

17:15:37
1306752

​Amurka Ta Sanya Jiragen Daukar Kaya Na Iran Cikin Jirin Takunkuman Tattalin Arziki

Gwamnatin shugaban Biden na kasar Amurka ta bada sanarwan kakabawa jiragen daukar kaya mallakin wasu kamfanoni a kasar Iran takunkuman tattalin arzikin saboda abinda ta kira sabawa takunkuman da ta dorawa kasar Rasha.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ma’aikatar kasuwanci ta kasar Amurka tana bada wannan bayanin a jiya Litinin. Ta kuma kara da cewa Jiragen daukar kaya ko Cargo samfurin Boeng 747 mallakin kamfanoni da kuma gwamnain kasar , wato Mahan Air, Qeshm Fars Air, da kuma Iran Air suna jigilar kayakin lantarki daga kasar Iran zuwa kasar Rasha wanda gwamnatin Biden ta haramta saboda yakin da Rasha ta fara a Ukraine.

Ma’aikatar kasuwancin Amurka ta kara da cewa a halin yanzu akwai jiragen sama 183 wadanda gwamnatin Amurka ta dorawa takunkuman a duniya daga ciki har da wadan nan jiragen Cargo na kasar Iran.

Gwamnatin Joe Biden dai a baka tana cewa tana son komawa kan yarjeniyar JCPOA na shirin nukliyar kasar Iran sannan ta ce tsohon shugaban kasar Amurka Donal Trump yayi kuskure da ya fice daga yarjeniyar, amma kuma bai sauya halin gwamnatin Trump dangane da iran ba ko kadan. Wanda ya tabbatar da cewa bai da anniyar farfado da yarjeniyar.

342/