Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

20 Satumba 2022

17:15:05
1306751

​Chadi: Ministan Harkokin Wajen Kasar Chadi Ya Yi Murabus Saboda Sabani Da Gwamnatin Kasar

Ministan harkokin wajen kasar Chadi Mahamat Zene Cherif ya ajiye mukaminsa a jiya Litinin bayan abinda ya kira sabani tsakaninsa da kuma gwamtanin Mahamat Idris Deby.

Tashar talabijin ta Aljaeerah ta kasar Qatar da nakalto Cherif yana fadar haka a shafinsa na twitter. Tsohon ministan ya bayyana cewa saw da dama akan aiwatar da al-amura wadanda suka shafi ofishinsa ba tare da tuntunbarsa ba. Daga nan ya fahinci cewa suna ne kawai shi ne ministan harkokin waje.

Tsohon ministan ya kara da cewa ya sauka ne saboda shirin ba’a sanar da shi mafi yawan shirin gwamnati na sulhuntawa da yan tawayen kasar wanda aka gudanar a kasar Qatar a cikin watan da ya gabata ba.

Cherif dan shekara 48 a duniya ya rike wasu mukaman gwamnatin kafin Mahamar Idris Debi ya nada shi ministan harkokin waje bayan da ya dare kan kujerar shugababancin kasar bayan mutuwat mahaifinsa a shekarar da ta gabata.

342/