Da yake amsa tambaya game da kasancewar babban mai shiga tsakani na Iran, Ali Bagheri Kani, a cikin tawagar shugaba Ebrahim Ra’isi zuwa New York, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran, Nasser Kan’ani, ya ce taron na MDD wata haduwa ce da za’a iya amfani da ita domin tattaunawa da sauren bangarorin da yarjejeniyar ta 2015 ta shafa.
Ya kara da cewa Iran za ta yi amfani da duk wata dama wajen bayyana ra'ayoyinta, kuma taron Majalisar Dinkin Duniya na daga cikin damar da ake da ita, inji shi.
Yau Litinin ne dai shugaban kasar ta Iran, Ebrahim Ra’isi, ya kama hanyar zuwa birnin New York na Amurka domin halartar babban taron MDD karo na 77.
342/