Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ABNA24
Laraba

14 Satumba 2022

07:10:30
1305610

Rahoto Cikin Hotuna / Tafiyar Mutanen Birnin Abdul Khan Domin Tarbar Maziyartan Arbaeen Na Imam Husaini As

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - ya kawo rahoton cewa,a daidai cikin ranekun watan Safar na shekara ta 1444, al'ummar birnin Alwan Abdul Khan da ke tsakiyar birnin Karkheh mai tazarar kilomita 70 daga kan iyakar Chezabeh, sun yi himma wajen hidimtawa maziyartan Arbaeen da liyafa a gidajensu da kuma gudanar da jerin gwano iri-iri, don hidimtawa masu ziyara Imam Husain As, A cikin wadannan jerin gwanon, baya ga tarbar maziyartan suna kuma gudanar da bada abinci na lokuta guda uku, karin kumallo da abincin rana da na dare, da gabatar da ruwa da shayi, da yin sallolin jam’i, tarukan makoki da jawabai na hangen nesa. Ana gudanar da jerin gwano na mutanen Abdol Khan duk shekara daga kwanaki 10 kafin Arbaeen zuwa kwana uku bayan Arbaeen.